Dan Majalisar APC Ya ba 'Yan Siyasa Shawara kan Mutanen da Suke Wakilta

Dan Majalisar APC Ya ba 'Yan Siyasa Shawara kan Mutanen da Suke Wakilta

  • Ɗan majalisar wakilai na jam'iyyar APC ya tunatar da ƴan siyasa kan sauke nauyin da ke kansu na mutanen da suke wakilta
  • Sulaiman Abubakar mai wakiltar Gummi/Bukkuyum ya buƙaci ƴan siyasa su taimakawa mutanensu ba sai sun jira zuwan lokacin zaɓe ba
  • Ɗan majalisar ya nuna cewa ya kamata ƴan siyasa su kasance masu yin adalci ga kowa da kowa a kodayaushe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Ɗan majalisar wakilai na APC daga jihar Zamfara, Sulaiman Abubakar, ya ba ƴan uwansa ƴan siyasa shawara.

Ɗan majalisar na jam'iyyar APC ya buƙaci ƴan siyasa ka da su jira sai lokacin zaɓe domin tallafawa mutanen da suke wakilta.

Dan majalisar APC ya ba 'yan siyasa shawara
Sulaiman Abubakar ya bukaci 'yan siyasa su taimaki mutanensu Hoto: Sulaiman Abubakar, Real Tajudeen
Asali: Facebook

Ɗan majalisa ya samu tarba a APC

Sulaiman Abubakar, mai wakiltar Gummi/Bukkuyum na jihar Zamfara, ya bayyana hakan ne a ƙarshen makon da ya gabata, cewar rahoton jaridar The Cable.

Kara karanta wannan

Zaben Ondo 2024: Mataimakin dan takarar PDP ya hango gagarumar matsala

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi jawabin ne a wani taron gangami da aka shirya domin yi masa maraba zuwa jam’iyyar APC, rahoton Vanguard ya tabbatar.

A watan Oktoba, ɗan majalisar ya fice daga PDP zuwa APC saboda abin da ya kira rikicin cikin gida da ya addabi jam'iyyar.

Wace shawara ya ba ƴan siyasa?

"Na yi mamakin tarbar da mutanena suka yi min saboda idan ka sauya sheƙa zuwa wata jam'iyya, ina tunanin wasu ba za su bi ka ba, amma a wannan karon gaba ɗaya garin ne ya biyo ni muka koma APC daga PDP. Wannan abin farin ciki ne."
"Saƙon da na gaya musu shi ne siyasa ta jama'a ce. Abu ne da ya shafi wakiltar mutane, yi wa jama'a abin da ya dace tare da yin adalci ga kowa da kowa. "
"Wannan shi ne saƙon da na ke gayawa ƴan siyasa a yankina. Hanyar ci gaba ita ce ba sai an jira lokacin zaɓe ya zo ba a raba kuɗi."

Kara karanta wannan

Ondo 2024: Abubuwan da ya kamata ku sani game da ɗan takarar gwamnan SDP

- Sulaiman Abubakar

Ganduje ya magantu kan APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi magana kan nasarorin da jam'iyyar ke ci gaba da samu a Najeriya.

Ganduje ya yi hasashen cewa yadda jam’iyyar APC ke ƙara samun karɓuwa a ƙasar nan alama ce da ke nuna za ta daɗe tana mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng