Rikicin siyasar Zamfara: Kanin Sheikh Ahmed Gumi ya zama dan majalisar tarraya a PDP

Rikicin siyasar Zamfara: Kanin Sheikh Ahmed Gumi ya zama dan majalisar tarraya a PDP

Rabon kwado, masu iya magana suka ce baya hawa sama, domin kuwa ko ya hau sama sai ya fado don kwado ya samu abinsa, wannan shine kwatankwacin abinda ya faru da guda daga cikin yayan marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, Sulaiman Abubakar Gumi.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sulaiman na daga cikin wadanda suka amfana da hukuncin da kotun koli ta yanke na soke dukkanin kuri’in da jam’iyyar APC ta samu a zaben 2019 tun daga matakin gwamna, zuwa Sanata, majalisar tarayya da majalisar dokoki ta jaha.

KU KARANTA: Buhari ya nada Farfesa Hamidu a matsayin shugaban asbitin koyarwa na ABU dake shika

Rikicin siyasar Zamfara: Kanin Sheikh Ahmed Gumi ya zama dan majalisar tarraya a PDP
Rikicin siyasar Zamfara: Kanin Sheikh Ahmed Gumi ya zama dan majalisar tarraya a PDP
Asali: UGC

Hukuncin kotu ya umarci hukumar zabe mai zaman kanta INEC data baiwa duk dan takarar da yazo na biyu a zaben da aka fafata a 2019 kujeran da duk wani dan APC ya lashe, sakamakon kuri’unsa haramtattu ne.

Hakan tasa Sulaiman, wanda kanine ga Dakta Ahmad Gumi, wanda ya tsaya takarar kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltar Gumi da Bukuyum ya tsinci dami a kala, rabona minallai tsuntsu daga sama gasashshe, sakamakon hukuncin kotun data karbe nasara daga hannun Bukuyum Umaru Jibo.

Rahotanni sun bayyana cewa saboda tsammanin rashin samun nasara tasa Sulaiman ko wani yakin neman zabe na kirki bai yi ba, ganin cewa jahar Zamfara jahace ta APC mai mulki, don haka yayi zamansa a mazuninsa dake Kaduna, amma yana amsa sunan dan takara.

Amma wannan sharia da aka ce sabanin hankali ce ta sauya akalar siyasar jahar Zamfara, saboda kwace kujerun APC ga PDP da ma duk wata jam’iyya data zamo ta biyu, a yanzu haka INEC ta sanya ranar 27 don mika ma dan PDP, Mutawallen Maradun shaidar samun nasara, da kuma 31 ga watan Mayu ga sauran wadanda suka samu nasara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng