Kananan Sana'o'i: Gwamna Zai Raba Tallafin Naira Biliyan 5

Kananan Sana'o'i: Gwamna Zai Raba Tallafin Naira Biliyan 5

  • Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya yunkuro wajen tallafawa mata masu ƙananan sana'o'i domin bunkasa tattalin arzikin jihar
  • Dikko Umaru Radda ya yi bayani ne yayin raba tallafi ga mata 7,000 da suka fito daga yankin Arewa maso Yammacin Najeriya a Katsina
  • Gwamnan ya ce gina mata wajen ba su jarin sana'o'i abu ne mai matukar muhimmanci wajen raya al'umma da haɓaka tattalin arziki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Gwamna Dikko Umaru Radda ya shirya domin gwangwaje matan Katsina da tallafin kudi har Naira biliyan 5.

Dikko Radda ya bayyana cewa zai samar shirin bunkasa ƙananan sana'o'in mata wanda hakan zai haɓaka tattalin jihar.

Gwamna Radda
Dikko Radda zai raba tallafi ga mata. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Asali: Facebook

Legit tattaro bayanai kan yadda za a raba tallafin ne a cikin wani sako da hadimin gwamna Radda, Ibrahim Kaulaha Muhammad ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya ba dalibin da ya gama jami'a da sakamako mafi kyau yana tallan ruwa aiki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna zai raba tallafin N5bn a Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta fara shirin raba tallafin Naira biliyan biyar ga mata domin farfaɗo da ƙananan sana'o'i a jihar.

Gwamna Dikko Umaru Radda ya bukaci matan shugabannin majalisa da kananan hukumomi su rika yin shirye shiryen tallafawa mata.

Yadda za a raba tallafi ga mata

Kwamishinar harkokin mata a jihar Katsina, Hadiza Abubakar ta ce za a tantance mata masu ƙananan sana'o'i domin amfana da shirin.

Hajiya Hadiza Abubakar ta ce ma'aikatar mata ta jihar za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin shirin ya samu kammaluwa.

An rabawa mata 7,000 tallafi a Katsina

Kungiyoyi sun raba tallafi ga mata 7,000 domin fara sana'o'i yayin da aka yi wani taro a jihar Katsina.

An ruwaito cewa an zakulo matan ne daga kananan hukumomi 186 da suke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

A wajen taron ne kuma gwamna Dikko Umaru Radda ya yi alkawarin fara shirin tallafawa mata da Naira biliyan biyar.

Kara karanta wannan

Matashi ya haɗa baki da yan bindiga don garkuwa mahaifiyarsa a Katsina

An tallafawa mata a jihar Imo

A wani rahoton, kun ji cewa uwargidan gwamnan Imo, Misis Chioma Uzodimma ta ba mata 1,575 tallafin kudi da kayan noma a shirinta na bunkasa rayuwar matan jihar.

Misis Chioma Uzodimma ta bayyana cewa shirin tallafawa mata 1,575 wata alama ce ta jajurcewarta na samar da damarmaki ga kowa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng