Rahoto kan Minista Ya Jawowa Gidan Jaridu Matsala, Matawalle Ya Nemi Diyyar N60bn

Rahoto kan Minista Ya Jawowa Gidan Jaridu Matsala, Matawalle Ya Nemi Diyyar N60bn

  • Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya maka wasu yan jarida a gaban kotu bisa zargin sun bata masa suna
  • Tsohon gwamnan Zamfara ya gurfanar da Shu’aibu Mungadi da Tijjani Ramalan a gaban kotu bisa zargin yada karya
  • Haka kuma ya bukaci kotu ta bi masa hakkinsa tare da neman a biya shi diyyar N60bn bayan danganta shi da ta'addanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya maka wasu fitattun yan jaridu a Arewacin kasar nan a gaban kotu.

Ya dauki matakin ne bisa zargin yan jaridun da wallafa labaran karya da cin zarafinsa a kan matsalar tsaron kasar nan.

Matawalle
Karamin Ministan tsaro ya maka yan jarida gaban kotu Hoto: Dr Bello Matawalle
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa karamin Ministan tsaro zai yi shari’a ne da fitatttun yan jaridar nan, Shu’aibu Mungadi da Tijjani Ramalan.

Kara karanta wannan

'Ta burge ni': Abin da Sheikh Kabiru Gombe ya ce a liyafar auren yar Kwankwaso

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bello Matawalle ya kai yan jaridu kotu

Jaridar The Guardian ta wallafa cewa karamin Ministan tsaro, Dr. Bello Matawalle ya zargi yan jarida da furta kalaman kage da ke barazana ga mutuncinsa a kafafen yada labaran da su ke aiki.

Baya ga yan jaridar, Matawalle ya shigar da kokensa kan kafafen yada labaran da mutanen ke aiki, Vision Media Services Ltd, Vision FM, Talabijin Farin Wata da Liberty Rediyo.

Dalilin Matawalle na kai yan jarida kotu

Tsohon gwamnan Zamfara kuma karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya na zargin yan jarida da bayyana shi a matsayin mai daukar nauyin yan ta'adda.

Dr. Bello Matawalle ya sha musanta zargin, inda ya jaddada cewa ya yi kokari matuka wajen kakkabe matsalolin rashin tsaro da ta addabi Zamfara.

An zargi Matawalle da alaka da ta'addanci

A baya kun ji cewa wasu matasan APC sun nemi gwamnatin tarayya ta gaggauta tsige karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle daga mukaminsa saboda zargin hadinsa da rashin tsaro.

Kara karanta wannan

Matasan APC sun tono shirin da ake yi a karkatar da hankalin gwamnatin Tinubu

Matasan sun gudanar da zanga-zanga a babban birnin tarayya Abuja, tare da ba jami'an hukumar tsaron farin (DSS) damar gudanar da binciken karamin Ministan domin tabbatar da gaskiya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.