"Ba Garambawul ba ne": Tsohon Ministan Buhari Ya Fadi Dalilin Tinubu Na Korar Ministoci

"Ba Garambawul ba ne": Tsohon Ministan Buhari Ya Fadi Dalilin Tinubu Na Korar Ministoci

  • Tsohon ministan wasanni a gwamnatin Muhammadu Buhari ya taso Shugaba Bola Tinubu a gaba kan yi wa majalisar ministocinsa garambawul
  • Solomon Dalung ya bayyana cewa Tinuba ƙara yawan ministocinsa kawai ya yi ba garambawul ba
  • Tsohon ministan ya yi nuni da cewa Tinubu ya kori wasu daga cikin ministocinsa ne saboda ba su da gata a gwamnatin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon ministan wasanni a gwamnatin Muhammadu Buhari, Solomon Dalung, ya caccaki shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Solomon Dalung ya bayyana cewa Tinubu ba garambawul ya yi wa majalisar ministocinsa ba, hasalima ƙara girmanta ya yi.

Dalung ya caccaki Tinubu
Solomon Dalung ya caccaki Shugaba Bola Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Barrister Solomon Dalung
Asali: Facebook

Tsohon ministan ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da jaridar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ministan Buhari ya ce kan Tinubu?

Solomon Dalung ya bayyana cewa shugaban ƙasan ƙara yawan ministocinsa ya yi ba garambawul ya yi ba a gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

'Yadda manufofin Tinubu za su amfani miliyoyin ƴan Najeriya,' minista ya yi bayani

Tsohon ministan na wasanni ya bayyana ministocin da aka kora, an sallame su ne kawai saboda ba su da wanda ya tsaya musu a gwamnatin Tinubu.

Ya kuma bayyana cewa waɗanda aka ba muƙaman sababbin ministoci, an jawo su ne domin a saka musu kan wahalar da suka yi a lokacin kamfen.

"A ra'ayinna abin da ya faru shi ne ƙara yawan ministoci ba garambawul ba. Kawai tsarin rage talauci ne na Tinubu domin jawo wasu daga cikin waɗanda suka yi masa wahala a lokacin yaƙin neman zaɓe."
"Babu wani abu mai kama da yin garambawul. Waɗannan ministocin da aka kora marasa uwa ne a bakin murhu shi yasa aka sallame su."
"Abin da ya faru kenan kawai. Babu wani garambawul a majalisar ministoci da aka yi."

- Solomon Dalung

Dalung ya caccaki Tinubu kan zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa sohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung ya caccaki jawabin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kan zanga-zanga.

Dalung, wanda ya riƙe kujerar minista a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya ce jawabin Shugaba Tinubu ba zai tsaida zanga-zanga ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng