‘Dan Takaran APC Ya Zarce PDP da Ratar Kuri’u 204, 000 a Zaben Gwamnan Jihar Ondo
- Gwamna Lucky Aiyedatiwa da magoya bayansa za su yi farin ciki da sakamakon zaben gwamnan jihar Ondo
- An lura APC ta samu kuri’u har sama da 300, 000 daga kananan hukumomi 15 da aka sanar da sakamakonsu
- A zaben jihar Ondo, ita kuwa jam’iyyar PDP ta na can baya da kuri’un da har zuwa yanzu ba su kai 100, 000 ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Ondo – Ana cigaba da samun labarin sakamakon zaben gwamnan jihar Ondo da aka yi a ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba.
Gwamna Lucky Aiyedatiwa wanda shi aka tsaida a matsayin ‘dan takaran jam’iyyar APC a zaben gwamnan Ondo ya yi gaba.
Rahoto ya zo daga Daily Trust cewa jam'iyyar APC ce ta ke gaba a zaben gwamnan jihar Ondo da hukumar INEC ta shirya jiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai girma Lucky Aiyedatiwa ya zarce sauran ‘yan takaran da suka shiga zaben gwamnan.
Bayanan da aka samu daga sakamakon da aka tattara ya nuna APC mai mulki ta yi gaba da ratar kuri'u fiye da 200, 000 a yanzu.
Kuri'u nawa APC ta samu zuwa yanzu a Ondo?
Zuwa yanzu Lucky Aiyedatiwa ya samu kuri’u 301, 113 wanda hakan ya tabbatar da cewa shi ya fi kawo yawan kuri’u da aka kirga.
Agboola Ajayi wanda yake rike da tutar jam’iyyar PDP shi ne na biyu a zaben na Ondo, kuma sun yi wa SDP, LP da irinsu NNPP nisa.
Zaben Ondo: PDP ta samu kuri'u 97, 000
Daga sakamakon da hukumar INEC ta sanar, jam’iyyar PDP ta na da kuri’u 97,051, watau an ba ta tazarar kuri’u akalla 204,062.
Kananan hukumomi uku ne kurum ba a sanar da sakamakonsu ba, rahotanni sun zo cewa INEC ta dakatar da tattara kuri’un dazu.
Da misalin karfe 12:35 na safiyar Lahadi aka fara tattara sakamakon zaben gwamnan.
Shugaban jami’ar tarayya da ke Lokoja a jihar Kogi, Farfesa Olayemi Akinwunmi shi ne babban malamin zaben gwamnan na Ondo.
'Dan takaran PDP ya hango magudi a Ondo
Dama tun kafin a yi nisa aka ji Agboola Ajayi ya na kukan cewa an shirya magudi a zaben da 'yan takara kusan 20 suka shiga.
Bayan ya kada kuri’arsa a karamar hukumar Ese Odo, tsohon mataimakin gwamnan ya zargi hukumar INEC da son kai a zaben.
Asali: Legit.ng