Bidiyon Yadda Aka Cafke Malamin Asibiti da Ke Yiwa ‘Yan Bindiga Magani a Katsina
- A wani sabon ci gaba da aka samu, jami'an tsaro sun cafke wani malamin asibiti da ke yiwa 'yan bindiga magani a jihar Katsina
- An rahoto cewa malamin asibitin suna Rabe, ya na jinyar 'yan bindigar da aka jiwa rauni a karamar hukumar Batsari da kewaye
- A zantawarmu da kungiyar masu harhada magunguna ta Najeriya (PSN) sun karyata cewa wanda aka kama dan kungiyarsu ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - Dubun wani likita mai harhada magunguna ya cika yayin da jami'an tsaro suka tsananta kai hare-hare kan 'yan ta'adda a jihar Katsina.
Rahoto ya nuna cewa jami’an tsaro a jihar Katsina sun kama mai harhada magungunan da ake zargin yana yiwa 'yan bindiga magani idan sun ji rauni.

Source: Getty Images
Katsina: An cafke likitan 'yan bindiga
Mai sharhi kan lamuran tsaro a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama ne ya wallafa labarin a shafinsa na X a daren ranar Juma'a, 15 ga Nuwamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zagola Makama ya wallafa bidiyon malamin asibitin, a lokacin da ya ke amsa tambayoyi daga jami'an tsaron da suka kama shi.
Rahoton Makama ya yi nuni da cewa ‘yan bindigar da malamin asibitin ke yiwa magani ne ke ake zargin suna addabar karamar hukumar Batsari da kewaye.
Wanda ake zargin, mai suna Rabe, an ce ya amsa laifin da ake zarginsa da shi na jinyar duk wani dan bindigar da ya jikkata a yankin.
Likitan 'yan bindiga ya amsa laifinsa
A cewar majiyoyin, ya yi ikirari cewa ya kan kai ziyara maboyar ‘yan ta’addan domin ba da kulawa ga wadanda suka samu raunuka yayin arangama ko farmaki.
An rahoto cewa Rabe ya shaida wa jami’an tsaro cewa, yana bayar da magunguna da kuma jinyar ‘yan bindigar a duk lokacin da suka samu raunuka.
An ce ayyukan da ya ke yi ne ke baiwa ‘yan bindigar damar murmurewa tare da ci gaba da gudanar da ayyukansu na ta'addanci a yankin.
Kalli bidiyon a nan:
Kungiyar PSN ta karyata rahoton Makama
Sai dai awanni da bullar wannan rahoto, kungiyar masana hardada magunguna ta Najeriya (PSN) ta bakin sakatarenta, Pharm Abdulkadir Hamza ta karyata wannan rahoto.
A zantawarmu da Pharm. Abdulkadir bayan fitar wata sanarwa, ya ce ko kadan wanda ke cikin bidiyon ba dan kungiyarsu ba ne, don haka bai kamata a jinginawa masu lamarin ba.
"Mun tuntubi majalisar koli ta masana harhada magunguna, sun tabbatar ba su san wani Rabe ba, kuma ba shi da wani lasisin zama masanin harhada magunguna."
Kungiyar PSN ta bukaci mawallafin labarin, da ya gaggauta janye wannan labarin kasancewar wanda aka kama ba likitan harhada magunguna ba ne, kuma ba shi da alaka da aikin.
Asali: Legit.ng

