'Yan Bindiga Sun Yi Ta'addanci, Sun Hallaka Tsohon Kansila Har Lahira

'Yan Bindiga Sun Yi Ta'addanci, Sun Hallaka Tsohon Kansila Har Lahira

  • Wasu ƴan bindiga da ake zargin ƴan ƙungiyar asiri ne sun hallaka wani tsohon kansila a jihar Ogun da ke yankin Kudu maso Yamma
  • Ƴan bindigan sun hallaka tsohon kansilan ne bayan sun harbe shi a kai lokacin da yake tafiya kan babur a ranar Juma'a
  • Rundunar ƴan sandan jihar Ogun ta tabbatar da kisan da aka yi wa marigayin a cikin wata sanarwa da ta fitar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ogun - Wasu ƴan bindiga da ake zargin ƴan ƙungiyar asiri ne, a ranar Juma’a sun harbe wani tsohon kansila a jihar Ogun.

Ƴan bindigan sun harbe Mutiu Akinbami ne a ƙaramar hukumar Abeokuta ta Arewa, a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

'Yan bindiga sun yi ta'asa a Ogun
'Yan sun hallaka tsohon kansila a Ogun Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar The Punch ta rahoto cewa an harbe Akinbami wanda aka fi sani da Egor a kai ne a lokacin da yake kan babur tare da ɗansa.

Kara karanta wannan

Zaben Ondo: Ana dab da fara zabe, 'yan daba sun farmaki 'yan PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka kai harin

Wata majiya mai tushe da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa ƴan bindigan sun harbe marigayin ne a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 6:30 na Yamma.

"Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:30 na yamma a tsakanin hanyar Brewery Bust Stop da mahaɗar Olomoore."
"Da alama maharan da ake zargin ƴan ƙungiyar asiri ne, sun biyo bayansa ne tun daga gidansa ne da ke cikin rukunin gidaje na Olomoore."
"Sun zo ne a wata mota ƙirar Toyota Hilux, kuma suna zuwa wajensa yana tafiya kan babur tare da ɗansa, sai suka buɗe masa wuta."

- Wata majiya

Ƴan sanda sun tabbatar da harin

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Ogun, SP Omolola Odutola, ta tabbatar da kisan a wata sanarwa da ta aikewa manema labarai ranar Asabar, rahoton PM News ya tabbatar.

Ta bayyana cewa DPO na yankin ya yi gaggawar tura tawagar ƴan sintiri zuwa wurin, sannan suka kai tsohon kansilan zuwa babban asibitin Ijaiye, inda likita ya tabbatar da mutuwarsa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun harbe mafarauta a Kaduna, sun yi awon gaba da Fulani

Sojoji sun daƙile harin ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yamma sun samu nasara kan ƴan bindiga a jihar Sokoto.

Dakarun sojojin sun yi nasarar daƙile harin da ƴan bindiga suka kai a Gatawa cikin ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng