Ma'aikata na Murna da Kudi Mai Tsoka, Gwamna Ya Dakatar da Biyan Sabon Albashi
- Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya fadi dalilin jinkiri da aka samu kan fara biyan mafi ƙarancin albashi
- Mai girma Eno ya tabbatar da cewa akwai ma'aikatan bogi da yawa a jihar da suka koma kasashen ketare
- Wannan na zuwa ne bayan ma'aikata na murna da Gwamna Eno ya amince da biyan mafi ƙarancin albashi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Akwa Ibom - Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta dage fara biyan mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata.
Gwamna Umo Eno ya tabbatar da dakatar da fara biyan mafi ƙarancin albashin har sai an kammala bincike.
Gwamnonin da za su biya fiye da N80,000
Gwamnan ya ce akwai ma'aikatan da suka bar jihar zuwa ketare ba tare da ajiye aiki ba, cewar rahoton Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan amincewa da biyan mafi ƙarancin albashin N80,000 makwanni kadan da suka wuce.
Gwamna Eno ya bi sahun gwamnan Rivers da Lagos da suka amince da albashin N85,000 ga ma'aikata.
Kamar gwamna Eno, gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah shi ma ya amince da biyan albashin N80,000.
Gwamna ya dakatar da biyan sabon albashi
Gwamna Eno ya ce dole gwamnatinsa za ta yi bincike domin sanin ainihin ma'aikata a jihar na gaskiya.
"Ina sane da cewa mafi yawan ma'aikata sun bar jihar Akwa Ibom zuwa wasu wurare a Najeriya inda wasu suka koma ketare."
"Dole mu tabbatar, mu kuma tantance ma'aikatan gaskiya a jihar Akwa Ibom domin bincikar na bogi."
"Dole mu tantance ma'aikatan bogi domin tabbatar da adalci a cikin tsarin kamar yadda gwamnatinmu ta himmatu wurin inganta ma'aikata."
- Umo Eno
Legit Hausa ta yi magana da wani ma'aikacin karamar hukuma a Gombe kan matakin Gwamna Eno Umo game da mafi ƙarancin albashi.
Abubakar Sadiq ya ce idan har za su samu albashin ba tare da zaftarewa ba jinkirin ba matsala.
Sadiq ya ce a Gombe sun ga jafa'i musamman ma'aikatan kananan hukumomi inda aka ba wasu N39,000.
Ya koka kan irin kudin mota da suke kashewa zuwa dangwala yatsa wanda a karshe yake cinye albashin gaba daya.
Gwamna Eno zai biya albashi 2 a Disamba
Kun ji cewa Gwamna Umo Eno ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta biya ma’aikatan Akwa Ibom albashi biyu a cikin Disamba.
Wannan albashi na “Eno-Mber” a cewar gwamnan zai taimaka wajen samar da farin ciki ga ma'aikata a lokutan bikin Kirsimeti.
Rahotonni sun nuna cewa gwamnan ya dauki matakin ne bayan jinkirin aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi da a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng