Tankar Gas Ta Yi Aman Wuta bayan Faduwarta a Jihar Arewa

Tankar Gas Ta Yi Aman Wuta bayan Faduwarta a Jihar Arewa

  • Jama'a a jihar Katsina sun shiga zullumi bayan wata tankar gas ta kife tare da kamawa da wuta nan take
  • Lamarin ya jawo asarar dukiyoyi da dama wanda har yanzu ba a kai ga tabbatar da adadin abubuwan da aka rasa ba
  • A bidiyon gobarar da aka wallafa a shafin sada zumunta, an gango wutar tankar gas din ta na tashi kololuwar sama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina - Wata tanka makare da iskar gas ta kife a jihar Katsina, inda aka ga wuta ta na tashi bayan tankar ta fashe.

Lamarin ya afku a yankin Magamar Jibia a karamar hukumar Jibia da ke jihar Katsina a lokacin da tankar ke tsaka da tafiya.

Kara karanta wannan

"Mun bar shi da halinsa:" Gwamnatin Tinubu za ta daina tankawa Atiku

Katsina
Tankar gas ta fadi a Katsina Hoto: Dr. Umaru Dikko Radda
Asali: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa jama'a sun shiga zullumi bayan an ga tankar dauke da iskar gas din girki ta kama da wuta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gobarar tankar gas ta jawo asara

Tanka dauke da gas da ta fadi a jihar Katsina ta jawo tarin asara da har yanzu ba a kai ga gano yawan abubuwan da aka rasa.

Wasu daga cikin abubuwan da wutar ta lalata sun hada da ababen hawa masu tarin yawa da wasu kadarorin da ake kokarin kayyade adadinsu.

Tankar gas ta fadi a jihar Katsina

Har yanzu hukumomi ba su yi bayani kan tankar gas da ta kama da wuta a Jibia da ke karamar hukumar Katsina ba.

Lamarin ya jawo gagarumar asara, yayin da ba a kai ga gano abin da ya haddasa faduwar tankar ba.

Tanka makare da gas ta fadi

A wani labarin kun ji cewa wata tanka cike da silindar gas din girki ta fadi a jihar Legas, kuma nan da nan hukumomi su ka kai agajin gaggawa domin ceto rayuka da dukiyoyi a yankin.

Kara karanta wannan

Rayukan matasa sun salwanta bayan ruftawar mahakar ma'adanai a Filato

Lamarin ya jefa jama'a cikin tsoro ganin hadarin irin kayan da tankar ke dauke da su, amma jami'an agajin hukumar kula da ababen hawa ta jihar Legas (LASTMA) ya kai daukin gaggawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.