Bello Turji da Mayakansa na Shan Luguden Wutan Kwanaki 4 a Jere
- Dakarun sojojin kasar nan na cigaba da artabu da mayakan Turji da su ka addabi Arewa maso Yammacin kasar nan
- Dakarun da ke samun taimakon yan sa kai na Gatawa sun shafe kwanaki hudu a filin kamar yadda mazauna su ka ambata
- Ana artabun ne bayan mayakan Bello Turji sun biyo jagoransu zuwa wani yanki na Sakkwato daga jihar Zamfara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Sokoto - Rundunar sojojin Najeriya ta rike wuta wajen lallasa mayakan yan ta'addan da ke karkashin jagorancin Bello Turji.
Turji ya yi kaurin suna wajen kai hare-haren ta'addanci jihohin da ke Arewa maso Yamma, musamman Sakkwato, Zamfara da Katsina.
BBC Hausa ta wallafa cewa mazauna yankin sun ce an shafe kwanaki ana musayar wuta tsakanin dakarun Najeriya da mayakan Turji.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana musayar wuta tsakanin sojoji da Turji
Wasu daga cikin mazauna jihar Sakkwato sun bayyana cewa sun gaza samun bacci na tsawon kwanaki hudu saboda rugugin wuta.
Wasu daga cikin mazauna yankin sun bayyana cewa wuraren da abin ya fi shafa sun hada da Tara, Gatawa, Kurawa da Daudama.
Sojoji sun tarfa mayakan Bello Turji
Wasu mazauna Sakkwato sun bayyana cewa karar bindigogi ya karade yankuna da dama yayin da ake artabu tsananin yan ta'adda da sojoji.
"Karar bindigogi za ka ji kamar mu na Gaza, abin babu dadi. Wajen kwanaki uku tun daga karfe 9.00 n.d za ka ji bindigogi na ta kara.
Wani daga Sakkwato ya ce wata bindigar idan aka harba, sai su ji kamar dakunansu za su ruguza.
Arangama ta kaure tsakanin Turji da sojoji
A baya kun ji cewa an samu rahotannin cewa rikici ya kaure tsakanin yan kungiyar sa kai da hadin gwiwar sojoji inda su ka yi ram da yan ta'adda masu mubaya'a ga Bello Turji.
Har yanzu ana artabun da aka fara tun kwanaki uku da su ka wuce, kuma zuwa wannan rana ta Juma'a ana cigaba da fafatawa a kokarin kawar da Turji da yaransa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng