Za a Faɗaɗa Filin Jirgin Muhammadu Buhari, Zai Fara Aiki a 2025
- Gwamnatin tarayya ta dauki aniyar fadada filin jirgin saman Muhammadu Buhari da ke jihar Borno domin inganta sufuri
- Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya ziyarci jihar Borno domin tabbatar da fadada filin jirgin saman a kan lokaci
- Rahotanni sun tabbatar da cewa za a yi haɗaka ne tsakanin gwamnatin tarayya da jihar Borno domin fadada filin jirgin saman
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Wakilan gwamnatin tarayya sun ziyarci jihar Borno domin fadada filin jirgin saman Muhammadu Buhari.
Ministan sufurin jiragen saman Najeriya, Festus Keyamo ne ya jagoranci tawaga zuwa birnin Maiduguri a makon nan.
Legit ta tatttaro bayanai kan yadda ziyarar ta kasance a cikin wani sako da Festus Keyamo SAN ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a fadada filin jirgin Muhammadu Buhari
Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya ziyarci jihar Borno a kokarin faɗaɗa filin jirgin saman Muhammadu Buhari.
Festus Keyamo ya bayyana cewa za a fadada filin jirgin saman ne domin ya fara jigilar kasa da kasa.
Yayin ziyarar, Keyamo ya samu rakiyar jami'an DSS, NDLEA, Kwastam, jami'an shige da fice inda suka gana da gwamna Babagana Umara Zulum.
"Ziyarar ta taimaka kan yadda za a fadada filin jirgin saman Muhammadu Buhari ya fara jigilar kasa da kasa.
Ana sa ran cewa aikin zai kammala zuwa watan Janairun 2025 kuma zai kawo cigaba a Arewa maso Gabas."
- Festus Keyamo
Gwamna Babagana Umara Zulum ya yi godiya ga Bola Ahmed Tinubu da Festus Keyamo bisa kokarin fadada filin jirgin.
Rahoton Channels Television ya nuna cewa Zulum ya ce jihar Borno za ta bayar da dukkan gudunmawa domin ganin shirin ya kammala.
Legas: Jirgin sama ya samu matsala
A wani rahoton, kun ji cewa jirgin sama na Air Peace ya gamu da tangarda a lokacin da yake shrin tashi daga birnin Abuja zuwa Legas da safiyar Alhamis.
Kamafanin sufurin jiragen saman Air Peace ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce jirgin ya fasa tashi sakamakon farmakin wata tsuntsuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng