Matashi Ya Haɗa Baki da Yan Bindiga don Garkuwa Mahaifiyarsa a Katsina

Matashi Ya Haɗa Baki da Yan Bindiga don Garkuwa Mahaifiyarsa a Katsina

  • Wani matashi a jihar Katsina ya hada baki da wasu yan bindiga wajen sace mahaifiyarsa, lamarin da ya ba mamaki matuka
  • Mutumin wanda zuwa yanzu ba a kai ga bayyana sunansa ba ya kuma nemi kudin fansa domin kashe mu raba da miyagun
  • Rundunar yan sandan jihar Katsina ba ce komai a kan batun ba duk da Legit ta tuntubi kakakin rundunar, ASP Abubakar Sadiq

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina - Wani matashi a Katsina ya tafka kuskuren da ya dauki hankalin jama'a wajen hada baki da yan bindiga.

Matashin, wanda ya ke mazaunin Kakia ne a Katsina ya nemi taimakon yan ta'adda wajen sace mahaifiyarsa.

Katsina
Wani ya haɗa baki wajen sace mahaifiyarsa Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa matashin ya aikata haka ne domin biyan wata bukatar kashin kansa.

Kara karanta wannan

Bello Turji da mayakansa na shan luguden wutan kwanaki 4 a jere

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Katsina: Matashi ya yi garkuwa mahaifiyarsa

Jama'a sun fusata bayan an bayyana mutumin da ya hada kai da miyagun yan ta'adda a jihar Katsina domin sace mahaifiyarsa.

Rahotanni sun bayyana cewa mutumin ya kuma nemi kudin fansa, duk da dai har yanzu babu cikakken karin bayani kan mummunan aikin.

Jama'a sun yi martani da jin labarin

Wasu fusatattun masu amfani da shafin X sun yi tir da wanda ya hada baki da yan bindiga wajen aikata aiki mafi muni ga mahaifiyarsa a Katsina.

Jama'a da dama sun yi mamakin yadda mutum mai cikakken hankali zai aikata irin wannan danyen aiki ba tare da jin komai a ransa ba.

@barkindo ya ce;

"Me yake faruwa ga matasan Arewa, mahaifiyarsa fa. Wannan abin takaici ne matuka."

@Usman1107341 ya wallafa cewa;

"Kalle shi, mara amfani."

@suleimar ya ce;

"Tsinanne

@UmarTUma ya wallafa cewa;

"A tura shi kabarinsa da wuri. Zai iya yi wa kowa.

Kara karanta wannan

'Dan China ya yaga kudin Najeriya a gaban mahukunta, an yi masa rubdugu a bidiyo

@Mariodafz4 ya ce;

Wace sana'a ce ta ke tafiya a Arewa ban da garkuwa da mutane.

Sojoji sun kashe yan bindiga a Katsina

A baya kun ji cewa dakarun sojojin kasar nan sun yi namijin aiki, sun fatattaki yan bindiga tare da kashe wasu daga cikinsu a harin da aka kai maboyar yan bindiga a Katsina.

Dakarun sojojin sama na Operation fansan yamma a ƙarƙashin Operation farautar mujiya na yankin Arewa maso Yamma, sun hallaka yan bindiga 15.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.