Rundunar Sojin Najeriya Ta Tura Dakaru Masu Yawa Zuwa Jihar Ondo, Bayanai Sun Fito
- Sojojin Najeriya sun tura jami'ansu zuwa Ondo domin tabbatar da tsaro a zaben gwamna na ranar Asabar, 16 ga Nuwamba
- 'Yan sanda za su jagoranci tsaro na cikin gida, yayin da sojoji za su taimaka wajen ganin an gudanar da zaben cikin lumana
- An sanar da takaita zirga-zirgar ababen hawa daga 6:00 na safe zuwa 6:00 na yamma domin tabbatar da tsaro a ranar zaben
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ondo - Rundunar soji ta sanar da cewa ta tura sojoji zuwa jihar Ondo domin tabbatar da tsaro a zaben gwamnan jihar na ranar Asabar, 16 ga Nuwamba.
An ce tura sojojin zai taimakawa rundunar 'yan sandan Najeriya, wadda su ke jagorantar tsaro na cikin gida a lokacin gudanar da zaben.
An tura sojoji Ondo domin ba da tsaro
Tuni dama 'yan sanda suka sanar da takaita zirga-zirgar ababen hawa a jihar daga karfe 6:00 na safe zuwa 6:00 na yamma a ranar zaben inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manjo-Janar Edward Buba, daraktan watsa labarai na hedikwatar tsaro ya ba da tabbacin cewa sojoji za su tabbatar an gudanar da zaben jihar cikin lumana.
Manjo Janar Buba ya bayyana cewa jami'an soji za su hada kai da 'yan sanda domin tabbatar da cewa zaben ya gudana ba tare da wata matsalar tsaro ba.
Gudunmawar sojoji a harkokin zabe
An ce tuni jami'an sojin saman Najeriya suka gudanar da jigilar kai kayayyakin zabe zuwa Ondo daga hedikwatar hukumar hukumar zabe ta kasa (INEC).
Punch ta rahoto sojoji za su kasance a wuraren zaben domin tabbatar da tsaron 'yan kasa, wanda hakan zai ba jama'a damar yin zabe ba tare da tsangwama ko barazana ba.
Bisa al'ada, sojin sama kan yi jigilar kayayyakin zabe yayin da sojojin kasa kuma kan taimakawa 'yan sanda wajen tabbatar da an yi zaben cikin tsaro.
Ondo: 'Yan daba sun farmaki 'yan PDP
A wani labarin, mun ruwaito cewa mutum shida daga cikin 'yan jam'iyyar PDP a jihar Ondo sun samu rauni bayan harin da wasu 'yan daba suka kai masu.
An ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba a karamar hukumar Idanre a wani taron siyasa, kimanin kwanaki biyu kafin zaben gwamnan jihar.
Asali: Legit.ng