'Na Hana Shi Muƙami ne': Ministan Tinubu Ya Tona Abin da Hada Shi Fada da Lauya
- Tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike ya tona ainihin abin da ya haɗa shi da fitaccen lauya, Deji Adeyanju
- Wike ya ce rana daya Adeyanju ya fara caccakarsa saboda ya nemi sahalewarsa a mukami a PDP bai amince ba
- Ministan ya ce saboda ba shi da aikin yi a yanzu, Adeyanju ya dawo dan gwagwarmaya da neman hakkin al'umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike ya fadi abin da ya haɗa shi faɗa da fitaccen lauya kuma mai kare hakkin al'umma, Deji Adeyanju.
Wike ya ce Adeyanju ya fara zaginsa ne bayan hana shi muƙami da ya yi a matsayin sakataren yada labaran PDP.
Nyesom Wike ya ce ya hana lauya mukami a PDP
Tsohon gwamnan Rivers ya fadi haka ne a jiya Laraba 13 ga watan Nuwambar 2024 yayin hira da yan jaridu a Abuja, Vanguard ta ba da rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wike ya ce Adeyanju ya tuntube shi domin ya shige masa gaba wajen samun muƙamin sakataren yada labaran PDP.
Ministan ya ce Adeyanju bayan rasa damar yanzu ya dawo dan gwagwarmaya inda yake caccakar gwamnatinsu kullum, cewar Daily Post.
Wike ya fadi yadda Adeyanju ya sauya
"Akwai wani yaro da suke kiransa Adeyanju, dan asalin jihar Kogi ne, ya same ni saboda yana neman muƙamin sakataren yada labaran PDP, na ce a'a."
"Na ce ba zai yiwu ba, kuma ba ni nadamar yin haka ko kadan, lokaci daya ya koma dan gwagwarmaya da neman hakkin al'umma saboda ba shi da aikin yi."
- Nyesom Wike
Wike ya magantu kan rikicin PDP
Kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike ya caccaki Gwamna Bala Mohammed kan rashin iya shugabanci da zai hada kan yan PDP.
Wike ya ce abin takaici ne kowa nema yake ya kassara shi, ya ce ba zai yi tasiri ba wurin shawo matsalolin jam'iyyar hamayyar ba.
Tsohon gwamnan ya ce babu yadda aka iya da shi saboda babu mahalukin da ya isa ya durkusar da shi kamar yadda suke zato.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng