Gwamnatin Tinubu Za Ta Raba Tallafin Dala Miliyan 134

Gwamnatin Tinubu Za Ta Raba Tallafin Dala Miliyan 134

  • Gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu za ta cigaba da shirin tallafawa manoma domin wadatar da Najeriya da kayan abinci
  • Ministan noma, Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka yayin kaddamar da shirin noman rani da za a yi a zangon 2024/2025
  • Sanata Abubakar Kyari ya ce gwamnatin tarayya ta karbo rancen makudan kudi daga bankin cigaban Afrika domin bunkasa noma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ma'aikatar noma da samar da abincin ta kasa ta yi bayani kan shirin ba manoma tallafi.

A cewar ma'aikatar, za a raba tallafin kudi ga manoma domin tabbatar da kowane dan Najeriya ya samu abinci.

Abubakar
Gwamnatin tarayya za ta raba tallafi ga manoma. Hoto: Sanata Abybakar Kyari
Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta wallafa cewa ma'aikatar noma ta ce gwamnatin Bola Tinubu za ta ba kimanin mutane 400,000 tallafin noma a zangon 2024/2025.

Kara karanta wannan

An bayyana ɓangarorin da Saudiyya za ta yi haɗaka da Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Tinubu za ta raba tallafin $134m

Gwamnatin tarayya ta karbo bashin kudi har $134m daga bankin raya Afrika domin ba manoma tallafi a Najeriya.

Ministan noma da samar da abinci, Sanata Abubakar Kyari ya ce za a raba tallafin ne ga waɗanda suke noma a rani da damuna.

Haka zalika za a raba tallafin ne a karkashin shirin gwamnatin tarayya na bunƙasa noma a Najeriya (NAGS-AP).

Dalilin raba tallafin noma a Najeriya

Ministan noma, Sanata Abubakar Kyari ya bayyana cewa shirin zai taimaka wajen samar da wadataccen abinci a Najeriya.

A karkashin haka, gwamnatin tarayya za ta mayar da hankali a kan noman alkama, masara, waken suya, rogo da sauransu.

Mutanen da za a ba tallafin noma

Sanata Abubakar Kyari ya bayyana cewa a zagayen farko na 2024/2025 za a ba mutane 250,000 tallafin noman alkama.

Haka zalika ya kara da cewa mutane 150,000 za a ba tallafin noman shinkafa a zagaye na biyu na zangon 2024/2025.

Kara karanta wannan

Gwamanti ta fara shirin karya farashin abinci, za a ba manoma tallafi

An fara noman zamani a Neja

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Neja ta kaddamar da noma da kayan aiki na zamani, ana fatan samun kayan abinci mai tarin yawa.

Gwamnan jihar, Umaru Muhammad Bago ya fara shirin noman ne a kokarinsa na samar da abinci da zai wadata yan Najeriya sosai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng