Zaben Ondo: Ana Dab da Fara Zabe, 'Yan Daba Sun Farmaki 'Yan PDP

Zaben Ondo: Ana Dab da Fara Zabe, 'Yan Daba Sun Farmaki 'Yan PDP

  • Mambobin jam'iyyar PDP sun fuskanci wani hari yayin da suke gudanar da taron siyasa a jihar Ondo da za a shirya zabe
  • Ana zargin wasu ƴan daba sun farmaki mambobin na PDP inda suka raunata mutum shida a ƙaramar hukumar Idanre
  • Rundunar ƴan sandan jihar wacce ta tabbatar da aukuwar harin ta bayyana cewa ta fara gudanar da bincike kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Ƴan daba sun farmaki mambobin jam'iyyar PDP yayin da suke gudanar da wani taro a jihar Ondo.

Rahotanni sun bayyana cewa aƙalla mambobin PDP shida ne aka kwantar a asibiti sakamakon farmakin da ƴan daban suka kai musu a ƙaramar hukumar Idanre ta jihar.

An kai hari kan mambobin PDP a Ondo
'Yan daba sun farmaki mambobin PDP a Ondo Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba a yayin wani taron siyasa.

Kara karanta wannan

Ondo 2024: Aiyedatiwa da wasu jerin ƴan takarar gwamna 3 da za su iya lashe zabe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Harin na zuwa ne kwanaki biyu kacal kafin gudanar da zaɓen gwamnan jihar.

An farmaki wasu 'ya 'yan jam'iyyar PDP a Ondo

Mai magana da yawun jam'iyyar PDP, Kennedy Peretei, ya tabbatar da faruwar harin, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

"Eh, wasu ƴan daba sun afkawa mambobinmu a Idanre. Wasu daga cikinsu yanzu haka suna kwance a asibiti."

- Kennedy Peretei

Duk da yake bai bayar da cikakken bayani game da harin ba, ya bayyana cewa ya faru ne a yayin wani taron siyasa a garin.

Me ƴan sanda suka ce kan harin?

A halin da ake ciki, rundunar ƴan sandan jihar Ondo ta ƙaddamar da bincike kan lamarin.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Funmilayo Odunlami-Omisanya, ta tabbatar da hakan, ta bayyana cewa kwamishinan ƴan sandan jihar, Oladipo Abayomi, ya kira taron sulhu da shugabannin manyan jam’iyyun siyasa.

Ta kuma sake nanata gargaɗin kwamishinan na cewa rundunar ƴan sanda ba za ta amince da duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya kafin zaɓe ko kuma bayan zaɓen ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun harbe mafarauta a Kaduna, sun yi awon gaba da Fulani

Gwamnatin Ondo ta ba da hutun zabe

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Ondo ta ayyana ranar hutu domin zaɓen gwamnan jihar da ke tafe a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamban 2024.

Gwamnatin ƙarƙashin jagorancin Gwamna Lucky Aiyedatiwa ta ayyana ranar Juma’a 15 ga watan Nuwamba a matsayin ranar hutu ga ma’aikatan jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng