"Ba 'Yan Najeriya ba ne": Nuhu Ribadu Ya Fadi Masu Amfana da Tallafin Fetur
- Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) ya bayyana amfanin cire tallafin man fetur da gwamnatin Bola Tinubu ta yi
- Nuhu Ribadu ya bayyana cewa ba ƴan Najeriya ba ne ke amfana da tallafin da gwamnati ta daɗe tana biya domin saukin man fetur ba
- Malam Ribadu ya nuna cewa cire tallafin ya kawo ƙarshen ayyukan fasa-ƙwaurin man fetur zuwa ƙasashen da ke makwabtaka da Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya yi magana kan cire tallafin man fetur da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi.
Nuhu Ribadu ya bayyana cewa cire tallafin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi, ya kawo ƙarshen fasa-ƙwaurin man fetur da ake yi zuwa ƙasashen waje.
Nuhu Ribadu ya bayyana haka ne a ranar Laraba a Abuja, a wajen taron da shugaban hukumar kwastam ya shirya, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Ribadu ya ce kan cire tallafin fetur?
Mai ba shugaban ƙasan shawara kan harkokin tsaron ya ƙara da cewa Najeriya na tallafawa ƙasashe makwabta ne kawai sakamakon fasa-ƙwaurin da ake yi ta iyakokin ƙasar nan.
Ya bayyana cewa ba ƴan Najeriya ba ne suke amfana da tallafin man fetur saboda fasa-ƙwaurin da ake yi.
"Na fito ne daga yankin kan iyaka, kuma a kullum ina yawan samun kiraye-kiraye kan yadda hukumar kwastam ke wahalar da masu fasa-ƙwauri."
"Abin mamaki mutanen da ke taimaka musu sun haɗa da sojoji amma yanzu komai ya wuce domin duk waɗannan Janar-Janar da jami’an tsaron da ke ba masu fasa-ƙwaurin man fetur kariya an sauya su da wasu sababbi."
"Haka nan tallafin da dukkanmu ke magana a kai wanda ya durƙusar da kamfanin NNPCL yana yi wa kasashe makwabta ne kawai amfani ba ƴan Najeriya ba."
"Muna ba da tallafi ga Nijar, Chadi, Burkina Faso, Kamaru, Jamhuriyar Benin, Ghana da kuma ƴan Najeriya masu wayo da suka kira kansu ƴan kasuwar man fetur."
- Nuhu Ribadu
Ribadu ya gargaɗi ƴan Lakurawa
A wani labarin kuma, kun ji cewa mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya yi magana da kakkausar murya kan ƴan ta'addan ƙungiyar Lakurawa.
Nuhu Ribadu ya gargaɗi ƴan sabuwar ƙungiyar da ke yankin Arewa maso Yamma cewa ƙarshensu ya kusa zuwa idan ba su daina ayyukan ta’addanci ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng