Zaben Ondo: Gwamna Aiyedatiwa Ya Ayyana Ranar Hutu

Zaben Ondo: Gwamna Aiyedatiwa Ya Ayyana Ranar Hutu

  • Gwamnatin jihar Ondo na ci gaba da shirye-shiryen tunkarar zaɓen gwamnan da ke tafe a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamban 2024
  • Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya ayyana ranar Juma'a, 15 ga watan Nuwamban 2024 a matsayin ranar hutu ga ma'aikatan gwamnatin jihar
  • An ba da hutun ne domin ba masu kaɗa ƙuri'a damar zuwa wuraren da suke yin zaɓensu ba tare da wata takura ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Gwamnatin jihar Ondo ta ayyana ranar hutu domin zaɓen gwamnan jihar da ke tafe.

Gwamnatin ƙarƙashin jagorancin Gwamna Lucky Aiyedatiwa ta ayyana ranar Juma’a 15 ga watan Nuwamba a matsayin ranar hutu ga ma’aikatan jihar.

Gwamnatin Ondo ta ba da hutu
Gwamnatin Ondo ta ba da hutu saboda zaben gwamna Hoto: Hon. Lucky Orimisan Aiyedatiwa
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren ofishin shugaban ma'aikatan jihar, Mista O.F. Ayodele ya fitar a ranar Laraba, cewar rahoton jaridar New Telegraph.

Kara karanta wannan

Gwamna a Arewa ya kinkimo aikin da zai laƙume Naira biliyan 20

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Gwamna Aiyedatiwa ya ba da hutu

A cewar sanarwar, an ba da hutun ne domin ba jama'a damar shiga cikin harkokin zaɓen wanda aka shirya gudanarwa ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba, 2024.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa hutun zai sauƙaƙawa masu kaɗa ƙuri’a zirgar-zirgar da za su yi.

Hakanan, zai taimakawa mutanen da suka cancanci kaɗa ƙuri'a zuwa rumfunan zaɓensu ba tare da tunanin zuwa wurin aiki ba.

Jam'iyyar APC mai mulki a jihar na daga cikin jam'iyyun da za su fafata a zaɓen da ke tafe na ranar Asabar.

Sakamakon zaɓen dai shi ne zai nuna wanda zai ja ragamar shugabancin jihar nan da shekara huɗu masu zuwa.

Gwamna Aiyedatiwa zai biya sabon albashi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya ce za a fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N73,000 ga ma’aikatan gwamnati daga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Ondo: Kotun ɗaukaka ƙara ta kori ɗan takarar gwamna kwanaki 2 gabanin zaɓe

Gwamna Aiyedatiwa ya ce walwala da jin daɗin ma'aikata na ɗaya daga cikin abubuwan da gwamnatinsa za ta fi ba fifiko.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng