Matasan APC Sun Tono Shirin da Ake Yi a Karkatar da Hankalin Gwamnatin Tinubu
- Matasan APC reshen Zamfara sun yi martani ga takwarorinsu na Kaduna da su ka jagorancin neman a tsige Bello Matawalle
- Kungiyar APC ta gudanar da zanga zanga a babban birnin tarayya Abuja, inda ta nemi a raba Bello Matawalle da mukaminsa
- Sun danganta neman a tsige karamin Ministan da tuhume tuhumen da ake yi masa na hannu a cikin cigaban ta'addanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara – Matasan jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara sun fusata bisa zanga zangar da wasu su ka gudanar a babban birnin tarayya Abuja, ana neman a tsige karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle.
Kungiyar matasan APC ta zargi mutanen da cewa makiya gwamnatin tarayya ne da ayyukan da ta ke yi a kasa.
Jaridar Leadership ta ruwaito kungiyar ta fadi haka a sanarwar da shugaban APC Youth Integrity Network, Idris Ibrahim ya fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matasan APC sun caccaki masu zanga zanga
Shugaban kungiyar, Idris Ibrahim ya ce wadanda su ka yi zanga zangar neman a tsige Bello Matawalle ba su da kishin kasa.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa kungiyar matasan APC a Zamfara ta fara zargin wasu da kokarin kawo nakasu a yaki da rashin tsaro.
An samu farraka tsakanin matasan APC
Kungiyar matasan APC ta Zamfara ta zargi takwararta ta Kaduna da cewa babu abin da ta iya sai jangwalo tashin hankali a jiharta.
Matasan Zamfara sun bayyana haka ne bayan shugaban kungiyar matasan APC na APC Akida ‘Forum’, Musa Mahmud ya nemi a tsige Bello Matawalle kan rashin tsaro.
Fadar shugaban kasa ta yi watsi da wadannan zargi ta bar tsohon gwamnan a ofis.
Kungiyar APC ta nemi tsige Matawalle
A baya kun ji cewa matasan APC sun dunguma zuwa babban birnin tarayya Abuja, inda su ka gudanar da zanga zanga su na bukatar shugaban kasa, Bola Tinubu ya tsige karamin Ministan tsaro.
Daruruwan matasan sun bayyana cewa zanga zangar ta zama dole duba da yadda ake zargin Dakta Bello Matawalle da hannu dumu-dumu a cikin rura wutar ta'addanci a jiharsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng