'Yan Bindiga Sun Harbe Mafarauta a Kaduna, Sun Yi Awon Gaba da Fulani

'Yan Bindiga Sun Harbe Mafarauta a Kaduna, Sun Yi Awon Gaba da Fulani

  • Miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi ta'asa a ƙauyen Kurutu da ke ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna
  • Ƴan bindiga sun hallaka wasu mafarauta biyu bayan sun yi musu kwanton ɓauna a lokacin da suke dawowa daga farauta
  • Bayanai sun ce tsagerun sun kuma sace wasu Fulani makiyaya tare da wani direban mota bayan sun dira a rugarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Wasu ƴan bindiga sun kai hari a jihar Kaduna inda suka hallaka mafarauta mutum biyu.

Ƴan bindigan sun kashe mafarautan ne a ƙauyen Kurutu da ke ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.

'Yan bindiga sun kai hari a Kaduna
'Yan bindiga sun hallaka mafarauta a Kaduna Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wani shugaban al’umma a yankin ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka kai harin

Ya bayyana cewa ƴan bindigan sun kai harin ne a ranar Litinin da ƙarfe 5:11 na safe.

Kara karanta wannan

An rasa rayuka bayan 'yan bindiga sun farmaki sojoji a wani shingen bincike

Shugaban al'umman ya ce mafarautan na dawowa ne daga farautarsu, kwatsam sai ƴan bindigan suka yi musu kwanton ɓauna a dajin da ke kan iyaka da ƙauyukan Kurutu da Azzara.

Ya ce ƴan bindigan sun buɗe musu wuta a nan take, ya ƙara da cewa an kwaso gawarwakinsu kuma an birne su.

Ƴan bindiga sun sace Fulani a Kaduna

Shugaban al’ummar, ya kuma bayyana cewa an yi garkuwa da makiyaya uku tare da direban motar ɗaukar kaya a ƙauyen Kurmin-Kare da yammacin ranar Talata a wata rugar Fulani da ke yankin.

Ya ce lamarin ya faru ne lokacin da direban motar ɗaukar kayan ya zo kai wasu shanu zuwa kasuwar ƙauyen SCC da ke yankin.

Ba a samun jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur, ba kan hare-haren guda biyu.

Wasu yan bindiga sun farmaki sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun kai farmaki a sansanin sojoji da safiyar ranar Laraba inda suka hallaka jami'an tsaro mutum biyu a jihar Abia.

Kara karanta wannan

'Yan Boko Haram sun zo da ta'addanci, sun yi barna a Borno

Ƴan bindigan sun kai harin ne a ƙauyen Ekenobizi a yankin Umuopara wanda ke kan iyaka da jihohin Imo da Abia.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng