Kamfanin Mai NNPCL Ya Yi Garambawul, Ya Kori Wasu Manyan Jami'ai

Kamfanin Mai NNPCL Ya Yi Garambawul, Ya Kori Wasu Manyan Jami'ai

  • Kamfanin NNPCL ya yi wasu ƴan sauye-sauye a tsakanin manyan jami'ansa domin inganta ayyuka da cika muradan ƴan Najeriya
  • A wata sanarwa ranar Laraba, NNPCL ya sallami manyan jami'ai biyu daga aiki sannan ya naɗa waɗanda za su maye gurbinsu nan take
  • Kamfanin man kasar ya naɗa Isiyaku Abdullahi a matsayin sabon mataimakin shugaban sashen kula da harkokin tace mai da rabawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Kamfanin mai na ƙasa watau NNPCL ya sanar yin wasu sauye-sauye a majalisar gudanarwa domin ƙara inganta ayyukansa.

NNPCL ya sauke Umar Ajiya daga matsayin babban jami'in kula da harkokin kudi da kuma Oritsemeyiwa Eyesan daga matsayin mataimakin shugaban sashin mai (EVC).

Shugaban NNPCL, Mele Kyari.
NNPCL ya yi sauye-sauye, ya sallami wasu kanyan ma'aikata Hoto: NNPC Limited
Asali: Facebook

Kamfanin NNPCL ya yi sauye-sauye

A madadinsu, NNPCL ya nada Isiyaku Abdullahi a matsayin sabon mataimakin shugaban sashin harkokin tace mai Udobong Ntia a matsayin EVC na sashen harkar haƙo ɗanyen mai.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun maida hannun agogo baya, sun kai hari tashar wutar lantarki a Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan sauye-sauye na kunshe ne a wata sanarwa da kamfanin NNPCL ya wallafa a shafin X ranar Laraba, 13 ga watan Nuwamba.

Haka nan kuma NNPCL ya kuma naɗa Adedapo Segun, tsohon mataimakin sashen tacewa da raba mai a matsayin babban jami'in kula da harkokin kudi.

Dalilin garambawul a kamfanin NNPCL

Sanarwar ta bayyana cewa an yi wannan sauye-sauye ne da nufin inganta ayyukan kamfanin mai na ƙasa.

"Waɗannan naɗe-naɗe sun yi daidai da kudirin NNPCL na haɗa tawagar nagartattun shugabanni domin bai wa mara ɗa kunya wajen sauke nauyin da ke kan kamfanin."
"Majalisar gudanarwa ta wannan kamfani na miƙa godiya ga Umar Ajiya da Oritsemeyiwa A. Eyesan bisa hidimar da suka yi wa kamfanin na tsawon lokaci," in ji sanarwar.

Kamfanin NNPCL ya kuma ƙara jaddada kudirinsa na yin aiki tukuru domin share hawaye da cika muradan ƴan Najeriya wanda sune mafi muhimmanci.

Kara karanta wannan

EFCC: 'Yadda wani gwamna a Najeriya ya tura miliyoyin Naira zuwa asusun ɗan canji'

Kyari: NNPCL ya daina shigo da man fetur

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kamfanin mai na ƙasa (NNPCL), Mele Kyari ya bayyana cewa sun daina shigo da tataccen man fetur daga ketare.

Kyari ya kuma musanta cewa NNPCL na nuna adawa ga matatun man cikin gida kamar matatar Alhaji Aliko Ɗangote da ke Legas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262