Ondo 2024: Laifuffukan Zabe da ke Jefa Yan Siyasa a Gidan Kurkuku
- Masu kada kuri'a da jam'iyyun siyasa sun kusa kammala shirin gudanar da zaben gwamnan jihar Ondo a ranar Asabar
- Dokar zabe ta shekarar 2022 ta tanadi wadansu tsare tsare da haramcin aikata wasu laifuffuka a zabukan kasar nan
- Dukkanin laifuffukan da dokar ta lissafa za su iya jefa mutum a gidan yari na tsawon shekaru, hakan zai danganta da girman laifin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Ondo – A ranar Asabar 16 Nuwamba, 2024 mazauna jihar Ondo za su sake zabar gwamna wanda zai yi wa’adin shekara hudu a kan mulki.
Tuni yan siyasa, musamman na jam'iyyyn APC, PDP da NNPP su ka dade a cikin shirin da su ke sa ran zai kawo masu nasara a zaben.
Legit ta wallafa cewa yayin da ake shirin zabukan, akwai wasu manyan laifuffuka da matukar hukumar INEC ta kama yan siyasa da su, akwai yiwuwar su shiga gidan yari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zaben Ondo: Laifuffukan da ke kai mutum zuwa kurkuku
1. Karya dokar rajistar zabe
Sashe na 114 (a zuwa f) na dokar zaben kasa ya jero abubuwan da ta bayyana a matsayin laifin yin rajistar zabe a siyasar Najeriya.
Laifuffukan sun hada da yin rajista sau biyu, shaidar rajista na bogi, sojan gona a matsayin jami’in yin rajista da makamantansu.
Hukuncin da aka tanada bisa aikata su sun hada da tarar N1,000,000 ko daurin watanni ko kuwa a hada duka.
2. Akwai laifufukan tsayar da dan takarar zabe
Sashe na 11 ya mayar da hankali kan hana duk wani laifi da hukumar ta ke ganin dan takara zai aikata kan tsayar da shi takara.
Dokar ta haramta samar da takardun tsayar da takara na bogi, samun dan takara da kuri’un bogi ko lalata akwatunan zabe da makamantansu.
An tanadi hukuncin daurin da bai gaza shekaru 10 ba ko tarar N50,000,000 ko hada dukkanin hukunce-hukuncen.
3. Tayar da tarzoma a tarukan siyasa/neman zabe
Sashe na 116 ya haramta kokarin tayar da husuma da tashe tashen hankula a lokacin zabe, kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa.
“Duk wani mutum da aka samu da tayar da tarzoma a wajen taron siyasa ko ya tunzura wasu aka aikata ba daidai ba domin kawo cikas kan taron da ake yi, ko aka same shi da makami, ya aikata laifin da za a yi masa daurin watanni 12 ko tarar N500,000 ko a hada duka biyun," cewar dokar.
Kotu ta kori 'dan takara a zaben Ondo
A wani labarin kun ji cewa kotun daukaka kara ta soke Olusola Ebiseni daga zama dan takarar gwamnan jihar Ondo a inuwar jam'iyyar LP yayin da a saura kwanaki kadan a yi zabe.
Kwamitin alkalai uku karkashin mai shari'a Adebukola Banjoko ce ta yanke hukuncin a zaman kotu na ranar Laraba, tainda ta bayyana gamsuwa da korafin jam'iyyar LP.
Muhammad Malumfashi, babban Edita a sashen Hausa, Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng