'Yan Bindiga Sun Maida Hannun Agogo Baya, Sun Kai Hari Tashar Wutar Lantarki a Arewa
- Kamfanin rarraba wuta TCN ya ce wasu ƴan bindiga sun kai farnaki sabuwar tashar wutar da ake ginawa a Obajana, jihar Kogi
- A wata sanarwa da kamfanin ya fitar a daren Talata, ya ce miyagun sun lalata na'urar raba wuta da aka riga aka kafa a wurin
- Wannan dai na zuwa ne daidai looacin da ƴan Najeriya ke fama da rashin yawan ɗaukewar wutar lantarki sakamakon lalacewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kogi - Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki sabuwar tashar wutar lantarki ta kamafanin wuta na ƙasa TCN a Obajana da ke jihar Kogi.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da shugaban sashin hulɗa da jama'a na TCN, Ndidi Mbah ya fitar a daren jiya Talata, 12 ga watan Nuwamba, 2024.
Jami'in ya ce maharan sun farmaki ƙaramar tashar raba wutar lantarki mai karfin 330/132/33kV da daddare a jihar da ke Arewa ta Tsakiya, in ji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan bindiga sun buɗe wuta a tashar TCN
Ndidi Mbah ya ce a rahoton da suka samu daga jami'an tsaron da ke wurin, ƴan bindigar sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi babu kaƙƙautawa.
Ya ce hakan ya tilastawa masu gadin wurin arcewa domin tsira da rayukansu a harin.
TCN: Ƴan bindiga sun yi ɓarna a Kogi
"A lokacin harin, sun lalata na'urar raba wutar lantarki mai karfin 150MVA 330/132/33kV da aka kafa a wurin, wanda hakan ya jawo lalacewar wasu abubuwa."
"Tuni kamfanin TCN ya fara kokarin tantance abubuwan da suka lalace da ɓarnar da maharan suka yi tare da haɗin guiwar ɗan kwangilar da ke aikin."
"Wannan hari wani ɓangare ne na yunƙurin lalata muhimman kayayyakin kamfanin wuta a faɗin ƙasar nan"
- Ndidi Mbah.
Kamfanin TCN dai na gina wannan sabuwar tsahar wutar lantarkin ne da nufin warware matsalar rashin hasken wuta a jihar Kogi da kewaye.
Wutar lantarki: Gwamnati na bukatar $10bn
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana buƙatar maƙudan kuɗi domin samar da wadatacciyar wutar lantarki a ƙasar nan.
Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya bayyana cewa ana buƙatar zuba hannun jarin $10bn kafin a riƙa samun lantarki ta tsawon sa'o'i 24 a kullum.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng