Basarake Ya Yi Magana da Ake Zarginsa da Kiran Mambobin PDP Su Farmaki Yan APC

Basarake Ya Yi Magana da Ake Zarginsa da Kiran Mambobin PDP Su Farmaki Yan APC

  • Rahotanni sun yi ta yawo inda ake zargin wani basarake da neman hada rigima tsakanin mambobin PDP da kuma yan APC
  • Ana zargin Oba Kayode Adenekan Afolabi da kiran mambobin PDP su kai farmaki kan yan jam'iyyar APC na reshen jihar Osun
  • Sai dai basaraken ya fitar da sanarwa inda ya musanta labarin tare da cewa shi mai son zaman lafiya ne kuma kowa ya sani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Osun - An yi ta yada jita-jita kan fitaccen basarake a jihar Osun saboda zargin hada APC da PDP fada.

Sarkin Apomu a jihar Osun, Mai martaba Kayode Adenekan Afolabi ya yi martani kan zargin da ake yi masa.

Basarake ya magantu kan zargin hada APC da PDP fada
Basarake a jihar Osun ya musanta hada APC da PDP fada. Hoto: Oba Kayode Adenekan Afolabi.
Asali: Facebook

Sarki ya musanta hada APC da PDP fada

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin Sarkin a bangaren yada labarai ya fitar, cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta tono zargin yadda APC ta shirya murɗe zaben gwamna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar, Afolabi ya musanta hannu a zargin neman hada rigima tsakanin jam'iyyun siyasa guda biyu.

Basaraken ya ce bai taba ingiza mambobin jam'iyyar PDP su farmaki yan APC ba a wani bidiyo da ake yaɗawa musamman a kafofin sadarwa.

Basarake ya fusata da neman bata masa suna

Sarkin ya ce babu inda a cikin faifan bidiyo ya yi magana kan zaben 2027 ko APC kamar yadda ake yi masa kazafi.

"Wannan labarin karya ne, babu inda na yi irin wannan magana, kawai an yada ne domin bata mani suna."
"Kowa ya sani ni mai son zaman lafiya ne, babu yadda zan yi ikirari ko goyon bayan tashin hankali."

- Oba Kayode Adenekan Afolabi

Rigimar sarauta ta barke a jihar Oyo

Kun ji cewa yayin da ake cigaba da rigima kan sarautar Ikoyi-Ile da ke karamar hukumar Oriire a jihar Oyo, kungiya ta ba gwamna shawara.

Kara karanta wannan

Bidiyo: NDLEA ta cafke kwayoyi a buhunan gyada, an gano kasar da za a kai su

Kungiyar ta bukaci Gwamna Seyi Makinde da ya sanya baki kan rigimar sarautar ka da ta koma wani abu daban musamman kawo rigimar da ba a yi tunani ba.

Hakan ya biyo bayan mutuwar Oba Abdul-yekeen Ayinla Oladipupo a 2022 da aka maye gurbinsa da wasu ke ganin ba a bi ka'ida ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.