Badakalar N27bn: Kotu Ta Shirya Yanke Hukunci a Shari'ar EFCC da Tsohon Gwamna
- Babbar kotun tarayya da ke babban birnin tarayya Abuja ta zauna a kan shari'ar hukumar EFCC da Darius Ishaku
- Mai shari'a Sylvanus Orji ya tanadi hukunci kan buƙatar da tsohon gwamnan ya shigar yana ƙalubalantar hurumin kotun
- Hukumar EFCC dai na tuhumar tsohon gwamnan kan zargin karkatar da N27bn daga asusun jihar Taraba da yake ofis
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tanadi hukunci a shari'ar hukumar EFCC da tsohon gwamnan Taraba, Darius Ishaku.
Alƙalin kotun mai shari’a Sylvanus Oriji, ya tanadi hukunci kan ƙalubalantar da tsohon gwamnan ya yi na cewa ba ta da hurumin sauraron ƙarar.
Jaridar Tribune ta rahoto cewa alƙalin kotun ya tanadi hukuncin ne a ranar Laraba, 13 ga watan Nuwamban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
EFCC na tuhumar tsohon gwamnan Taraba
Hukumar EFCC ta gurfanar da Darius Ishaku ne tare da tsohon babban sakataren ma'aikatar ƙananan hukumomi da masarautun jihar, Bello Yero.
An gurfanar da su a gaban kotun kan tuhume-tuhume 15 da suka shafi karkatar da N27bn.
Alƙalin kotun ya tanadi hukuncin ne bayan ya saurari jawaban da ɓangarorin suka yi kan buƙatar da waɗanda ake ƙara suka shigar na ƙalubalantar hurumin kotun na sauraron ƙarar, rahoton The Nation ya tabbatar.
Mai shari'a Sylvanus Oriji ya ce matakin da ya ɗauka na tanadar hukunci a shari'ar ya yi daidai da sashe na 396(3) na dokar gudanar da shari’ar laifuffuka (ACJA).
Karanta wasu labaran kan EFCC
- Badakalar N1.3trn: Tsohon gwamna ya yi martani kan gayyatar da EFCC ta yi masa
- Yahaya Bello: Matasan APC sun ba tsohon gwamna shawara kan takaddamarsa da EFCC
- EFCC ta gano abubuwa 3 da suka jawo wutar lantarkin Najeriya ke yawan lalacewa
EFCC ta gurfanar da tsohon gwamna a kotu
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaƙi da rashawa watau EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku a babbar kotun Abuja kan tuhumar zamba.
EFCC ta gurfanar da Ishaku tare da tsohon babban sakataren ma'aikatar kananan hukumomi da sha'anin masarautu a Taraba, Bello Yero gaban mai shari'a Sylvanus Oriji.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng