Abin da Yariman Saudiyya Ya Faɗawa Bola Tinubu kan Cire Tallafin Mai da Wasu Tsare Tsare

Abin da Yariman Saudiyya Ya Faɗawa Bola Tinubu kan Cire Tallafin Mai da Wasu Tsare Tsare

  • Yariman ƙasar Saudiyya, Muhammad Bn Salman ya yabawa tsaren-tsaren tattalin arzikin shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
  • A wata ganawa da suka yi bayan taron ƙasashen Musulunci da Larabawa, Bn Salman da Tinubu sun tattauna a Saudiyya
  • A cewar Yariman Saudiyya mai jiran gado, ya ɗauki irin matakan da Tinubu ya ɗauka a lokacin da ya zama Firaminista

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Saudi Arabia - Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Muhammad Bn Salman ya yabawa shugaban ƙasa Bola Tinubu bisa matakan da ya ɗauka na farfaɗo da tattalin arziki.

Muhammad Bn Salman ya yabawa shugaban Najeriya bisa tsare-tsaren da ya ɓullo da su tun bayan hawansa kan madafun ikon da nufin ceto tattalin arzikin ƙasa.

Bola Tinubu da yariman Saudiyya.
Yariman Saudiyya ya yabawa manufofin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafin X.

Kara karanta wannan

An bayyana ɓangarorin da Saudiyya za ta yi haɗaka da Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yariman Saudiyya ya gana da Bola Tinubu

Basaraken ya ce yariman ya jinjinawa shugaba Tinubu a wurin wata ganawa da suka yi bayan taron ƙasashen Larabawa da Musulunci wanda ya gudana ranar Litinin.

Shugaba Tinubu dai ya cire tallafin man fetur kuma ya canza tsarin hada-hadar musayar Naira ta yadda kasuwa ce za ta yanke farashin kudin Najeriya.

Waɗannan dai su ne manya tsare-tsaren da gwamnatin Tinubu ta bullo da su, waɗanda a cewarta duk da suna da raɗaɗi a farko, nan gaba ƴan Najeriya za su more.

Abin da Yariman Saudiyya ya faɗawa Tinubu

Da yake bayanin yadda ganawar Tinubu da Yariman Saudiyya ta kasance, Onanuga ya ce shugabannin sun tattauna kan inganta alaƙar ƙasashen biyu.

Ya ce Tinubu da Muhammad sun tattauna kan bangarorin hadin gwiwa kamar man fetur da iskar gas, noma, samar da ababen more rayuwa da dokokin kasuwanci.

Kara karanta wannan

Ana cikin surutun Musuluntar da Najeriya, Tinubu ya dawo Abuja daga taron Saudiya

Onanuga ya ce:

"Yarima mai jiran gado ya yabawa sauye-sauyen tattalin arziki na Shugaba Tinubu, ya yi nuni da kamanceceniya da matakan da ya dauka na karfafa zaman lafiya da ci gaban Saudiyya a lokacin da ya zama Firaminista.”

Bola Tinubu ya dawo gida daga Saudiyya

A wani rahoton, an ji cewa Bola Tinubu ya dawo Najeriya bayan halartar taron kasashen Larabawa da Musulunci a Riyadh, birnin kasar Saudiyya.

A filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, ministoci da shugaban APC suka tarbi shugaba Bola Tinubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262