Lakurawa Sun Ji Ruwan Alburusai, Sun Fara Guduwa daga Najeriya

Lakurawa Sun Ji Ruwan Alburusai, Sun Fara Guduwa daga Najeriya

  • Rundunonin tsaron kasar nan sun durfafi tarwatsa kungiyar yan ta'addan Lakurawa da su ka kutso Najeriya
  • Dakarun sojan sama da na kasa sun yi wa Lakurawan da ke da sansani a Kebbi ruwan wuta har su ka kora su
  • Rahotanni sun bayyana cewa yan ta'addan sun samu mafaka a kudancin jihar Kwara da ke iyaka da kasar Benin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kebbi - Mayakan kungiyar yan ta'addan lakurawa sun hadu da fushin hukumomin tsaron Najeriya yayin da ake korar fatattakarsu daga kasar.

Dakarun sojan kasa na shirin Operation Fansan Yamma da na sama da ke karkashin Farautar Mujiya sun hadawa Lakurwa zafi a jihar Kebbi.

Nigeria
Sojoji sun farmaki Lakurawa a Kebbi Hoto: HQ Nigerian Army/Nigerian Airforce HQ
Asali: Facebook

Jaridar Zagazola Makama ta tattaro cewa an yi wa Lakurawa taron dangi, aka rika kai masu hare-hare a shirin da rundunonin tsaron Najeriya ke yi na hallaka su.

Kara karanta wannan

Lakurawa sun fara firgita jama'a, gwamnatin Tinubu ta fadi matakan da ta dauka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumomin tsaron kasar nan ta bakin Minista tsaro, Muhammad Badaru Abubakar sun tabbatar da cewa ba za su yi wa Lakurawa sauki ba.

Lakurawa sun fara guduwa daga Kebbi

Jaridar The Cable ta wallafa cewa dakarun sojin sama da na kasan Najeriya sun kora yan ta'addan Lakurawa da ke da sansani a sassan Kebbi.

Harin da aka kai kan sansanin mayakan ya sa sun fara guduwa zuwa iyakar Benin da jihar Kwara bayan ruwan wuta ya fi karfinsu.

An kwato kayan 'yan ta'addan Lakurawa

Rundunonin tsaron kasar nan sun yi nasarar kwace shanu da wasu kayayyakin da aka kama a sansanin Lakurawa bayan an farmake su.

Rahotanni na bayyana cewa akwai yiwuwar wadanda aka kora su nutsa kudancin jihar Kwara, wurin Ilesha Bariba inda za su kara haduwa.

Masani ya ba hukuma shawara kan Lakurawa

A wani labarin kun ji yadda guda daga cikin masu fafutukar kare hakkin bil'adama, Abdu Bulama Bukarti ya shawarci gwamnatin Najeriya ta zage damtse kan Lakurawa.

Kara karanta wannan

An bayyana ɓangarorin da Saudiyya za ta yi haɗaka da Najeriya

Barista Abdu Bukarti ya bayyana cewa kungiyar a shirye ta ke domin kaddamar da mugayen ayyukanta a kan yan kasar nan, sannan su na da ra'ayi tsatstsaura mai kama da na Boko Haram da ISWAP.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.