Matatar Ɗangote Ta Shimfidawa Ƴan Kasuwa Zabi 2, Sun Rage Farashin Litar Fetur
- Kungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu watau IPMAN ta ce za a rage N50 a farashin kowace lita a Najeriya
- Shugaban IPMAN, Abubakar Maigandi ya ce da zaran ƴan kasuwa sun fara sayen fetur daga matatar Ɗangote, za su sauke farashi
- Wannan dai na zuwa ne awanni kaɗan bayan IPMAN da matatar Ɗangote sun cimma matsayar fara kasuwanci a tsakaninsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ƴan kasuwa sun sanar da shirinsu na sauke farashin litar man fetur a faɗin Najeriya sa'o'i 24 bayan kulla yarjejeniyar kasuwanci da matatar Ɗangote.
Ƙungiyar dillalan mai masu zaman kansu watau IPMAN ta sanar da cewa ƴaƴanta za su rage N50 a farashin lita idan suka fara sayen mai daga matatar Ɗangote.
Shugaban IPMAN na ƙasa, Abubakar Garima ne ya bayyana hakan a wata hira da gidan talabijin na Channels tv ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matatar Ɗangote ta kulla yarjejeniya da IPMAN
Abubakar Garima ya ce matatar man Dangote ta amince za ta bai wa yan kungiyar IPMAN man fetur kowace lita a farashin N990 a manyan wurin ajiya da kuma N940 a motoci.
Bisa haka, Abubakar Garima ya ce, ‘yan kasuwa da a halin yanzu suke sayar da kowace litar man fetur N1,150 zuwa N1,200 za su rage farashin da N50.
"A yanzu an ba mu zaɓi guda biyu daban-daban kan yadda za mu sayi man fetur daga matatar Ɗangote.
"Na farko za mu iya ɗaukar kaya a motoci zuwa wuraren ajiyarmu a farashin N940. Na biyu kuma zamu iya saye a manyan wuraren ajiya a farashin N990."
IPMAN ta rage N50 a dalilin matatar Ɗangote
Shugaban IPMAN ya ba da misali da Maiduguri da ke Arewa maso Gabas, inda ya ce idan aka tafi a wannan tsarin farashin lita zai sauka daga N1,200 zuwa 1,150.
A ruwayar Tribune, Abubakar ya ce:
"A yanzu da nake magana a Maiduguri, ana sayar da litar mai N1,200, bisa wannan sauyi da aka samu za a iya rage farashin zuwa N1,150, ka ga an samu sauƙin N50, mai yiwuwa ma a rage abin da yafi haka."
NNPCL ya daina shigo da man fetur
Kun ji cewa shugaban kamfanin mai na ƙasa (NNPCL), Mele Kyari ya bayyana cewa sun daina shigo da tataccen man fetur daga ketare
Kyari ya kuma musanta cewa kamfanin NNPCL na nuna adawa ga matatun man cikin gida kamar matatar Alhaji Aliko Ɗangote.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng