Ana Batun Lakurawa a Arewa, Sojoji Sun Yi Wa 'Yan Bindiga Raga Raga
- Dakarun sojoji sun samu gagarumar nasara kan ƴan bindigan da suka yi yunƙurin kai hari a ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto
- Sokoto na rundunar Operation Fansn Yamma sun yi wa ƴan bindigan raga-raga waɗanda ake zargin sun fito ne daga sansanin Bello Turji
- Ɗan majalisar da ke wakiltar Sabon Birni 1 a majalisar dokokin jihar Sokoto ya tabbatar da nasarar da gwarazan dakarun sojojin suka samu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Dakarun sojoji na rundunar Operation FANSAN YANMA sun samu nasara kan ƴan bindiga a jihar Sokoto.
Dakarun sojojin sun yi nasarar daƙile harin da ƴan bindiga suka kai a Gatawa cikin ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto ranar Talata.
Ɗan majalisar dokokin jihar Sokoto mai wakiltar Sabon Birni 1, Aminu Boza, ne ya tabbatar da hakan, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojojin Najeriya sun ragargaji ƴan bindiga
Aminu Boza ya ce lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Talata, 12 ga watan Nuwamban 2024, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.
Ɗan majalisar ta bayyana cewa dakarun sojojin sun yi wa ƴan bindigan mummunar ɓarna waɗanda ake zargin sun fito daga sansanin Bello Turji ne da ake nema ruwa a jallo.
"Eh, sojoji sun dakile harin da ƴan bindiga suka kai a Gatawa, amma rashin sabis ba i bari na samu cikakkun bayanai ba."
"Amma daga bayanan farko da na samu, sojojinmu sun ragargaje su sosai."
- Aminu Boza
Wani babban jami’in runduna ta takwas a hedkwatar sojoji da ke Sokoto, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce irin wannan farmakin ba sabon abu ba ne ga sojoji.
Sojoji sun sheƙe ƴan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin saman Najeriya sun hallaka ƴan ta'adda masu yawa a wasu dazuzzukan da ke tsakanin jihohin Zamfara da Kebbi.
Rahotanni sun bayyana cewa ƴan ta’addan, waɗanda wasu daga cikinsu ƴan ƙungiyar Lakurawa ne, an kashe su ne a wani wuri da ake kira Sangeko a Zamfara, kusa da kan iyaka da jihar Kebbi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng