Lakurawa Sun Firgita Jama'a, Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Matakan da Ta Dauka
- Gwamnatin tarayya ta ce a shirye ta ke ta kakkabe kungiyar Lakurawa da su ka fara tsorata mazauna Arewacin kasar nan
- Ministan tsaro, Muhammadu Badaru Abubakar ya bayyana cewa tuni aka fara fitar da matakan da za su dakile tasirinsu
- Arewacin Najeriya da ke fama da matsalar yan ta'adda da yan bindiga ta sake samun kanta a cikin barazanar Lakurawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce yan Najeriya su kwantar da hankulansu bayan bullar sabuwar kungiyar yan ta'addan Lakurawa.
Kungiyar yan ta'addan ta ja hankulan manyan Arewa da sauran masu gwagwarmaya a yankin, inda ake nemi gwamnatin tarayya ta dauki matakin gaggawa.
A tattaunawar da ta kebanta da BBC Hausa, Ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar ya ce hukumomin tsaro ba za su zura ido su na kallon Lakurawan ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matakan dakile kungiyar Lakurawa
Ministan tsaron Najeriya, Muhammad Badaru Abubakar ya ce rundunar sojin kasa ta fara tattaunawa da jami'anta da ke bakin daga kan Lakurawa.
Ya ce ana duba yiwuwar kara yawan sojoji a jihohin da sabuwar kungiyar yan ta'addan ke da karfi tare da hana su yaduwa zuwa sassan Arewa ta Yamma.
Gwamnati ta nemi addu'o'i yakar Lakurawa
Gwamnatin tarayya ta ce akwai wasu karin matakan da ba ta bayyana ba, wadanda aka sa a gaba domin kakkabe Lakurawa kafin su yi karfi.
Ministan tsaron Najeriya, Muhammad Badaru Abubakar ya bukaci addu'o'in yan kasa, domin a cewarsa hakan zai taimakawa kokorin dakarun sojoji.
Lakurawa: Tsohon kyaftin ya ba da shawara
Kyaftin Abdullahi Adamu Bakoji mai ritaya ya shaidawa Legit cewa kungiyar Lakurawa ba ta zo da wani sabon salon ta'addaci da ba a taba ganin irinsa ba.
Bakoji ya yi takaicin yadda aka siyasantar da batun tsaro da da bullar kungiyoyin yan ta'ada da su ke barna a Arewa.
Ya ce idan gwamnati ta yi da gaske, za ta iya kakkabe ayyukan kungiyar kafin ta'addancinsu ya yi kamari.
An fadi shirin Lakurawa a Najeriya
A baya mun ruwaito cewa lauya mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Abdu Bulama Bukarti ya ce yan ta'addan Lakurawa sun dade a Najeriya, domin sun shafe shekaru shida.
Ya bayyana cewa yanzu haka sun karbe iko da daga wasu masu rike da sarautun gargajiya a kananan hukumomin jihar Kebbi, amma mahukunta sun karyata cewa an yi haka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng