Gwamanti Ta Fara Shirin Karya Farashin Abinci, za a ba Manoma Tallafi
- Gwamnati ta nuna damuwa kan samun tashin farashin kayan abinci a kasuwannin Najeriya wanda hakan ke zama barazana
- Ma'aikatar noma ta shirya taro na musamman a jihar Cross River domin samar da mafita wajen kawo karshen yawan tashin farashin abinci
- Babban sakataren ma'aikatar noma, Temitope Fashedemi ya ce an shirya taron ne domin nazari kan tsare tsaren gwamnatin tarayya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Cross River - Ma'aikatar noma ta kasa ta shirya taro na musamman a kan samar da wadataccen abinci a fadin Najeriya.
Sakataren ma'aikatar noma da samar da abinci, Temitope Fashedemi ya ce an shirya taron ne domin nazari kan wasu tsare tsaren gwamnatin tarayya a kan harkokin noma.
Ma'aikatar yada labarai ta kasa ta wallafa abubuwan da taron ya mayar da hankali a kai a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a ba manoma tallafi a Najeriya
Temitope ya bayyana cewa noma na cikin manyan ɓangarori kuma jagora wajen farfaɗo da tattalin Najeriya.
A karkashin haka, Fashedemi ya ce gwamnati za ta cigaba da hada kai da masu ruwa da tsaki wajen samar da abinci, da ba manoma da masu nazari kan noma tallafi.
Ma'aikatar ta ce hakan zai taimaka wajen jan hankalin sauran al'umma su shiga harkar noma gadan gadan a Najeriya.
Gwamanti ta damu da tashin farashin abinci
Temitope Fashedemi ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta damu da rahotonni da ta ke samu kan tashin farashin kayan abinci a Najeriya.
Fashedemi ya bayyana cewa saboda damuwar da suka yi kan lamarin ne aka shirya taron domin samo hanyar karya farashin abinci a kasar nan.
Nazarin tsare tsaren gwamntin Bola Tinubu
Temitope Fashedemi ya bayyana cewa daga cikin dalilan taron akwai sake nazari kan wasu tsare tsaren da Tinubu ya kawo a kan noma.
Ya kara da cewa za su samar da hanya da ta fi dacewa wajen samar da wadataccen abinci a Najeriya da samar da ayyukan bayan nazarin.
An fara noman zamani a Neja
A wani labarin, mun ruwaito muku cewa gwamnatin jihar Neja ta kaddamar da noma da kayan aiki na zamani a damunar bana inda ake fatan samun kayan abinci mai tarin yawa.
An ruwaito cewa gwamna Umaru Muhammad Bago ya fara shirin noman ne a kokarinsa na samar da abinci da zai wadata yan Najeriya sosai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng