Laifin Lakurawa Ya Shafi Fulani, An Kashe Mutane 6 a Kebbi
- Miyetti Allah ta koka bisa kisan wasu Fulani da ake zargin su ne su ka kai hari garin Mera a Juma'ar da ta gabata
- Mutane 15 ne su ka rasu a harin, wanda daga baya aka bayyana cewa yan ta'addan Lakurawa ne su ka kai shi
- Sakataren Miyetti Allah a Kebbi, Abubakar Lamido ya ce su kansu Lakurawan sun hana su sakat, domin su na kwace masu dabbobi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kebbi - Kungiyar makiyaya ta Miyetti reshen jihar Kebbi ya ya yi Allah-wadai da kisan Fulani shida wanda ake zargin an yi a harin ramuwar gayya.
Miyetti Allah ta zargi yan sa kai da kai farmaki kan Fulanin, inda su ka dora alhakin kisan mutane 15 da yan ta'addan Lakurawa su ka yi a kansu.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Miyetti Allah ta nesanta Fulani da harin Mera da aka kai a ranar Juma’ar da ta gabata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lakurawa: Miyetti Allah ta koka kan kisan Fulani
Jaridar Independent Newspaper ta ruwaito cewa kungiyar Miyetti Allah ta koka bisa yadda aka kashe Fulani a harin ramuwar gayya a Kebbi.
Sakataren kungiyar reshen jihar Kebbi, Abubakar Lamido ya bayyana cewa haka kuma an yi wa Fulanin da babu ruwansu ta’adi mai tarin yawa.
An zargi jama’a da lalata rugar Fulani
Sakataren Miyetti Allah a Kebbi, Abubakar Lamido ya bayyana cewa wasu yan kungiyarsa kai sun kona rugage akalla 185 tare da kona rumbun abinci 42.
Ya bayyana cewa an kai harin bisa kuskure domin su kansu Fulanin su na fama da harajin yan kungiyar Lakurawa da ke kwace masu kudi, dabbobi da karbar zakka daga gare su.
Lakurawa sun kashe mutum 15 a Kebbi
A baya mun ruwaito cewa an yi taho mu gama tsakanin mazauna jihar Kebbi da yan kungiyar yan ta’addan Lakurawa da ta fara bayyana kanta a jihar Kebbi, inda aka kashe mutane da dama.
Rahotanni sun bayyana cewa an yi kazamin fadan ne lokacin da yan Lakurawa su ka kai hari Mera da ke karamar hukumar Augie, inda mutane 15 su ka rasa rayukansu a kauyen tare da jikkata wasu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng