Abinci da Sufuri: Jerin Muhimman Abubuwa 9 da Suka Fi Cin Kuɗin Ƴan Najeriya

Abinci da Sufuri: Jerin Muhimman Abubuwa 9 da Suka Fi Cin Kuɗin Ƴan Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Galibin ƴan Najeriya sun daina kashe-kashen kuɗi barkatai sakamakon halin tsadar rayuwar da ake ciki a halin yanzu tun bayan cire tallafin mai.

Mafi akasarin magidanta sun yi wa kansu karatun ta natsu, suna kashe kuɗin da suke samu daga albashi ko sana'o'i wajen sayen abubuwan da suka fi zama dole.

Rayuwa a Najeriya.
Yadda yan Najeriya ke rayuwa a halin tsadar rayuwar da suka tsinci kansu Hoto: Contributor
Asali: Getty Images

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa akalla rabin ƴan Najeriya ba su iya ajiyar wasu kudi a asusu saboda yawan buƙatu da kuma tsadar kayayyaki.

A wani rahoto da PiggyVest ta wallafa, kaso 43% na ƴan Najeriya ba su iya ajiyar ko sisi a asusunsu na bankuna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta duba muhimman abubuwa tara da mutane suka fi maida hankali wajen sayensu a wannan shekara da ta fara yi mana bankwana watau 2024.

1. Abinci da kayan haɗi

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta fadi hanyar samun wadatacciyar wutar lantarki a Najeriya

Abincin da za a ci a kowace rana shi ne abu na farko da ya fi cin kudin magidanta a Najeriya, ga tsadar kayayyaki ga kuma ƙarancin kuɗin shiga.

Bincken ya nuna sama da mutum miliyan 100 a Najeriya sun wayi gari cikin ƙunci saboda albashi ko kuɗin shigar da suke samu a wata ba su iya ɗaukar ɗawainiyar iyalansu.

Cire tallafin man fetur da tallafin Naira na cikin tsare-tsaren gwamnati mai ci da ake ganin su ne sanadin ƙaruwar yunwa a ƙasar.

Hauhawar farashin kayan abinci ya sa ƴan Najeriya na kashe kaso 83% na abin da suke samu a wata wajen sayen abinci da za su sa a bakin salati na yau da kullum

Duk da tsadar da kayayyaki suka yi, mutane sun fi bai wa batun abinci fifiko fiye da komai.

2. Harkokin Sufuri

Kuɗin sufuri na ɗaya daga cikin abubuwan da ke ɗaukar kaso mai tsoka na kudin ƴan Najeriya musamman ma'aikata da masu sana'ar tafiye-tafiye.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito kan saukar dusar ƙanƙara a ɗakin Ka'aba

Yawancin ’yan Najeriya na zuwa aiki, makaranta, ko wasu wurare, suna kashe kusan rabin abin da suke samu wajen biyan kudin sufuri ko man feturin ababen hawa.

Wani malamin makaranta a Katsina, Bashir Ahmad ya shaida wa Legit Hausa cewa tsadar sufuri na ɗaya daga cikin abin da ke ci masu tuwo a ƙwarya.

Ya ce albashinsa na watan Oktoba ya kare ne a kan titi wajen zuwa tantancewa da gwamnati ta kirkiro, sannan ya koka kan rashin aiwatar da sabon albashi.

3. Kudin wuta da ruwa

Batun hasken wuta, ruwa da kuma sayen datar shiga yanzar gizo na ɗaukar wani kaso daga cikin kasafin kudin ƴan Najeriya na wata.

Kimanin kashi 38% na kudin shiga na wata-wata na ƙarewa ne a wajen biyan kudin wutar lantarki, man janareta, da sauran hidimomin gida da ake bukata.

4. Tsaftar jiki da tufafi

Duk da halin babun da ake ciki, har yanzu tufafi na cikin muhimman abubuwan da ke a sahun gaba a wurin galibin ƴan Najeriya musamman matasa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun hallaka wani bawan Allah ana saura ƴan kwanaki ɗaurin aurensa

Bincike ya nuna mutane kan ware kusan 35% na abin da suka samu wajen kula da tufafin da suke sa wa, tsaftar jiki da yanayin shigarsu.

Sannan suna amfani da wannan kaso wajen ɗinka kayan da ya dace idan za su halarci tarukan al'adu, zamantakewa, ɗaurin aure da sauransu.

5. Kula da yara a wurin magidanta

Kula da yara yana da mahimmanci ga yawancin magdanta musamnan masu aiki a Najeriya.

An tattaro cewa galibi magidanta kan kashe kusan kashi 24% na kudadensu wajen bai wa yara kulawa, biyan ƴan aiki da sauransu.

6. Kuɗin haya ko gyaran gida

An yi ƙiyasin cewa kudin kula da matsuguni kamar kudin hayar gida da kulawa, na ɗaukar kimanin kashi 23% na kasafin kuɗin mafi yawancin iyalai a wata.

Kudin haya ga ma'aikata ko magidantan da ke zaman haya abu ne da ake bukata a kowane wata ko a ƙarshen shekara.

A wani ɗan bincike da Legit Hausa ta yi, ta gano cewa yadda abubuwa suka tashi a Najeriya haka kudin haya suka karu a mafi yawan birane.

Kara karanta wannan

"Ba a fahimce ni ba," Sanata Sani ya faɗi alherin cire tallafin man fetur a Najeriya

Wani ma'aikacin gwamnatin tarayya da ya yi aure kwanan nan kuma ya tare a Zaria, kusa da inda yake aiki ya shaida mana cewa N550,000 ya kama gidan da yake zaune.

7. Kiwon lafiya

Sha'anin lafiya da ciwo wani abu ne da ke faɗowa a kowane lokaci, babu wanda ke sanin yaushe ne zai kwanta rashin lafiya.

An tattaro cewa galibin ƴan Najeriya na kashe akalla kashi 18% na albashi ko kuɗin da suke samu a wata wajen kula da lafiyarsu da ta iyalansu.

8. Neman ilimi

Ilimi na da matuƙar muhimmanci a Najeriya kuma duk da tsadar kudin makaranta, galibin iyaye na saka batun ilimi a sahun farko.

Ƴan Najeriya musamman magidanta ko mu ce iyaye suna ganin bai wa ƴaƴansu ilimi tamkar gina gobensu ne.

Ana hasashen magidanta na ware akalla kashi 14% na abin da suke samu wajen biyan kudin makaranta, sayen kayan makaranta da sauransu.

Kara karanta wannan

'Ku tsaya gida, ku bar fita kasar waje,' Tinubu ya aika sako ga matasa masu digiri

9.Taimakon ƴan uwa

A mafi yawan al'adun Najeriya, taimakon ƴan uwa wani abu ne mai muhimmanci musamman a wannan hali na kunci da ake ciki.

Kusan kashi 11% na kudin shiga a wata na tafiya ɓangaren taimakawa dangi, ko ta hanyar kuɗi, taimakon gaggawa, ko tallafi ga iyaye ko kakanni tsofaffi.

Tsadar fetur: Mutane sun canza dabara a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa hauhawar farashin man fetur ya tilastawa mazauna Kano amfani da kekuna, baburan lantarki ko tafiya a kasa.

Rahoto ya nuna cewa an samu karancin motoci a kan titunan jihar Kano yayin da jama'a ke neman saukin tsadar rayuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262