Ana cikin Surutun Musuluntar da Najeriya, Tinubu Ya Dawo Abuja daga Taron Saudiya

Ana cikin Surutun Musuluntar da Najeriya, Tinubu Ya Dawo Abuja daga Taron Saudiya

  • Shugaba Bola Tinubu ya dawo Najeriya bayan halartar taron kasashen Larabawa da Musulunci a Riyadh, birnin kasar Saudiyya
  • A filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja, Femi Gbajabiamila, ministoci da shugaban APC suka tarbe Shugaba Tinubu
  • A taron, Tinubu ya bayyana goyon bayan Najeriya ga tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Falasɗinu, tare da buƙatar mafita ta lumana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja bayan ziyararsa zuwa Saudiya inda ya halarci taron kasashen Larabawa da Musulunci.

An ce Bola Tinubu ya dura sashen shugaban ƙasa na filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja da misalin ƙarfe 8:00 na yammacin ranar Talata.

Femi Gbajabiamila, Ganduje da ministoci sun tarbi Tinubu bayan dawowarsa daga Saudiya
Tinubu ya duro Abuja bayan dawowa daga taron kasashen Musulunci da Saudiya. Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Bola Tinubu ya dawo Najeriya daga Saudiya

Wadanda suka tarbi Tinubu sun hada da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, tare da wasu manyan jami’an tsaro inji rahoton Channels.

Kara karanta wannan

An yi rashi: Tsohon alƙalin Kotun Koli ya kwanta dama, Tinubu ya tura sako

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika, ministoci kamar Nyesom Wike (babban birnin tarayya) da Wale Edun (kuɗi da tattalin arziki) suna cikin waɗanda suka je tarbar.

An ce akwai shugaban jam’iyyar APC mai mulki, Abdullahi Ganduje, a tawagar wadanda suka tarbi Shugaba Bola Tinubu a filin jirgin.

Shugaba Tinubu ya nemi tsagaita wuta a Gaza

Taron, wanda Sarki Salman da yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman suka shirya, ya tattauna batutuwa masu muhimmanci game da yankin Gabas ta Tsakiya.

A jawabinsa a taron, Tinubu ya jaddada kiran Najeriya na tsagaita wuta nan take kan rikicin Isra'ila da Falasɗinu da ya ki ci ya ki cinyewa, inji rahoton NTA.

Shugaba Tinubu ya tabbatar da goyon bayan Najeriya ga mafita ta ƙasashen biyu, domin ba Isra'ilawa da Falasɗinawa damar rayuwa cikin aminci da daraja.

Ya ba da shawarar kafa ofishi na musamman domin aiwatar da kudurorin taron kuma ya buƙaci shugabanni su samar da hadin kai na ƙasa da ƙasa.

Kara karanta wannan

Ana surutun musuluntar da Najeriya, Tinubu ya zauna da Yarima Mohammed a Saudiyya

Kalli bidiyon a nan kasa:

An soki Tinubu kan zuwa Saudiya

A wani labarin, mun ruwaito cewa Cif Charles Udeogaranya ya gargadi Bola Tinubu kan wakiltar Najeriya a taron kasashen Larabawa da na Musulmi a Saudiya.

Tsohon dan takarar shugaban kasar ya bayyana cewa shugaba Bola Tinubu ya take dokar kasa a halartar taron da ya yi domin Najeriya ba musulmar kasa ba ce.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.