Matawalle: Zanga Zangar Neman Bincikar Minista Ta Barke a DSS, An Samu Bayanai

Matawalle: Zanga Zangar Neman Bincikar Minista Ta Barke a DSS, An Samu Bayanai

  • Ƙungiyar APC Akida Forum ta gudanar da zanga-zanga a hedkwatar hukumar tsaron farin kaya a birnin tarayya Abuja
  • Ƴan jam'iyyar ta APC sun gudanar da zanga-zangar ne domin neman hukumar ta binciki ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, kan zargin alaƙa da ƴan bindiga
  • Ƙungiyar ta ce rashin bincikar zarge-zargen da ake yi wa Bello Matawalle zai yi wa APC, shugaba Bola Tinubu da hukumomin tsaro baƙin fenti

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar APC Akida Forum, ta gudanar da zanga-zanga a hedkwatar hukumar DSS da ke Abuja a ranar Talata.

Ƙungiyar ta buƙaci a gudanar da bincike tare da yiwuwar dakatar da ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, bisa zarginsa da alaƙa da ƴan bindiga.

An yi zanga-zanga kan Matawalle
'Yan APC sun yi zanga-zangar neman a binciki Bello Matawalle Hoto: Dr. Bello Matawalle
Asali: Twitter

Ƙungiyar da ke da hedkwata a jihar Kaduna, ta bayyana matuƙar damuwarta game da tsaron miliyoyin ƴan Najeriya musamman mazauna jihar Zamfara, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Asalin Lakurawa da shirin da sojojin Najeriya suka yi na kawo karshen ƴan ta'addan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa ƴan APC ke son a binciki Matawalle

Ƙungiyar ta bukaci hukumar DSS da ta gudanar da bincike kan manyan zarge-zargen da gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yi kan Bello Matawalle, rahoton Premium Times ya tabbatar.

Gwamna Dauda Lawal ya zargi magabacinsa, Bello Matawalle da daukar nauyin ƴan bindiga da karkatar da kuɗaden jihar.

Sun bayyana damuwarsu cewa rashin bincikar zarge-zargen na iya ɓata ƙimar jam’iyyar APC, shugaban ƙasa Bola Tinubu da hukumomin tsaro.

Da yake jawabi yayin zanga-zangar, shugaban ƙungiyar Malam Musa Mahmud ya bayyana cewa so suke yi DSS ta binciki Bello Matawalle.

"Muna son hukumar DSS ta ƙaddamar da bincike na ƙashin kanta kan ɗimbin zarge-zargen da ake yi wa ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle."
"Hukumar DSS za ta iya ba shugaban ƙasa shawara ya sauke Bello Matawalle daga muƙaminsa domin ya fuskanci kwamitin bincike."
"Dole ne ministan ya fayyace alaƙarsa da mutane masu hatsari irinsu Bello Tagoji, Musa Kamarawa, da Ardon Zuru."

Kara karanta wannan

Lakurawa: Abubuwan sani dangane da sabuwar kungiyar 'yan ta'adda da ta bullo a Arewa

- Malam Musa Mahmud

Ministan Tinubu ya samu yabo

A wani labarin kuma, kun ji cewa jagoran jam'iyyar APC kuma shugaban ƙungiyar PAPSD, Dakta Sani Shinkafi, ya yabawa ƙaramin ministan tsaro Bello Matawalle.

Dakta Sani Shinkafi ya yabawa ministan kan nasarorin da aka samu a yaƙin da ake yi da ƴan bindiga a jihar Sokoto.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng