Gwamnatin Kano Ta Runtumo Bashin Biliyoyin Naira daga Ƙasar Faransa? Gaskiya Ta Fito

Gwamnatin Kano Ta Runtumo Bashin Biliyoyin Naira daga Ƙasar Faransa? Gaskiya Ta Fito

  • Gwamnatin Kano ta musanta raɗe-raɗin da ake cewa ta karɓo rancen Naira biliyan 177 daga wani mai bada lamuni a Faransa
  • Darakta janar na ofishin kula da basussuka, Dr. Hamisu Sadi Ali ya ce Gwamna bai karbo rancen ko sisi ba tun da ya hau mulki a 2023
  • Hamisu Sadi Ali ya ce maimakon haka ma gwamnati mai ci ta biya wani kaso a bashin da ta gada daga gwamnatin Abdullahi Ganduje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Gwamnatin jihar Kano ta fito fili ta musanta ikirarin cewa ta ciyo bashin N177bn daga hannun wani mai ba da lamuni a ƙasar Faransa.

Datakta janar na ofishin kula da basussuka na jihar Kano, Dr. Hamisu Sadi Ali ne ya karyata raɗe-raɗin da yake zantawa da manema labarai ranar Talata.

Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Gwamnatin Kano ta musanta karɓo rancen N177bn daga kasar Faransa Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Gwamnatin Kano ba ta ci sabon bashi ba

Kara karanta wannan

Gwamna ya bayyana gaskiya kan tashin bam a babban birnin jihar Arewa

Dr. Hamisu Sadi Ali ya ce gwamnatin Kano ba ta karɓo rancen ko kwandala ba tun da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya hau mulki a watan Mayu, 2023, kamar yadda Leadership ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun farko wasu kafafen yaɗa labarai sun wallafa rahoton cewa Gwamna Abba ya cimma matsayar karɓo bashin makudan kudi daga wani mai bada lamuni ɗan Faransa.

Da yake ƙarin haske kan lamarin, Hamisu ya ce bashin da ake surutu a kai ya samo asali ne daga yarjejeniyar lamuni da aka yi a 2018 a lokacin gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.

Da gaske gwamnatin Kano ta karɓo N177bn?

"Babu wani sabon bashi da aka karɓo, dukkan basussukan da muke fama da su a yanzu gadarsu aka yi daga tsohuwar gwamnatin da ta shuɗe.
"Gwamnatin Ganduje ta karɓo wani bashin Yuro miliyan 64 daga wata hukuma a Faransa domin yin aikin ruwa, kuma tuni aka bayar da Yuro miliyan 13."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba ta fadi basussukan da ta biya wadanda ta gada wajen Ganduje

- Hamisu Sadi Ali.

Hamisu Sadi Ali ya ƙara da cewa gwamnatin Abba ta fi maida hankali wajen rage bashin da ake bin jihar Kano, inda aka biya N63.5bn a 2024.

Gwamna Abba ya gabatar da kasafin 2025

A wani rahoton, an ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf gabatar da.kasafin kudin shekarar 2025 a gaban majalisar dokokin jihar Kano.

A kasafin kudin Kano na 2025, Abba Kabir Yusuf ya fifita bangaren ilimi da kaso mafi tsoka inda ya ce hakan zai kawo cigaba a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262