'Kin Biyan Sabon Albashi': Jigo Ya Fadi Babban Laifin da Wasu Gwamnoni Ke Aikatawa

'Kin Biyan Sabon Albashi': Jigo Ya Fadi Babban Laifin da Wasu Gwamnoni Ke Aikatawa

  • Shugabannin kwadago a Najeriya sun soki jihohin da suka ki aiwatar da sabon albashi, suna cewa hakan rashin adalci ne
  • Tsohon shugaban ƙungiyar kwadago, Ayuba Wabba, ya ce da zarar shugaban kasa ya saka hannu, to albashin ya zama doka
  • Ƙungiyar Kwadago ta Najeriya ta yi alƙawarin ɗaukar mataki a kan gwamnoni da ke ƙin aiwatar da sabon albashin N70,000

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Shugabannin ƙungiyar kwadago a Najeriya sun soki jihohin da ke jan kafa wajen aiwatar da mafi ƙarancin albashi na N70,000.

A cewar shugabannin kwadagon, kin biyan ma'aikata sabon albashin take hakkin ɗan Adam ne a wannan yanayi na matsin tattalin arziki.

Ayuba Wabba ya yi magana kan gwamnonin da suka ki aiwatar da sabon mafi karancin albashi
Shugabannin kwadago sun caccaki gwamnonin da suka ki fara biyan sabon albashin N70,000. Hoto: @NLCHeadquarters
Asali: Twitter

Ayuba Wabba ya magantu kan sabon albashi

Tsohon shugaban ƙungiyar kwadago, Ayuba Wabba, ya bayyana hakan a zantawarsa da sashen Hausa na BBC, inda ya gargadi gwamnonin kan laifin da suke aikatawa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya naɗa sabon SSG, ya ba ɗan tsohon shugaban APC babban muƙami

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamared Ayuba Wabba ya ce ce da zarar shugaban kasa ya sa hannu kan dokar mafi ƙarancin albashi, to kuwa albashin N70,000 ya zama doka.

Wabba ya bayyana cewa lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya sa hannu kan dokar, ta fara aiki nan take kuma tana shafar kowane rukuni na ma’aikata a ƙasar.

An koka da wasu gwamnonin Najeriya

Tsohon shugaban na NLC ya ƙara da cewa wasu jihohi sun riga da sun aiwatar da sabon albashin, inda jihar Borno ta sanya malaman makaranta a tsarin albashin.

A gefe guda, Wabba ya koka kan yadda wasu jihohi suka ki nuna wata alama ta lokacin da za su aiwatar da sabon albashin ba, lamarin da ya kira rashin mutunta dan Adam.

Ayuba Wabba ya yi nuni da cewa, kowa na sane da irin wahalhalun tattalin arziki da ake ciki Najeriya, kuma ma’aikata sun jure tsadar rayuwa na tsawon lokaci.

Kara karanta wannan

'Ka hana Wike, gwamnoni ba alkalai motoci da gidaje,' SERAP ta fadawa Tinubu

NLC za ta dauki mataki kan gwamnoni

Ƙungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta yi alƙawarin ɗaukar matakan da suka dace a kan gwamnoni da ke ƙin aiwatar da sabon albashin.

NLC ta zargi wasu gwamnoni da rashin tausayi, tana mai cewa ma’aikata sun cancanci girmamawa da kuma samun isasshen albashi na aikinsu.

NLC za ta tsunduma yajin aiki

A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta yi magana kan rashin aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi a wasu jihohin ƙasar nan.

NLC ta umarci 'ya'yanta a jihohin da har yanzu ba su fara aiwatar da sabon albashin ba, da su tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani, daga 1 ga watan Disamba, 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.