EFCC Ta Gano Abubuwa 3 da Suka Jawo Wutar Lantarkin Najeriya Ke Yawan Lalacewa
- Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa cin hanci da rashawa ne ya jawo ake samun cikas a samar da wutar lantarki
- Olukoyede ya ce yawancin 'yan kwangilar samar da lantarki na amfani da kaya marasa inganci, wanda ke jawo lalacewar wutar
- Hukumar ta nemi hadin gwiwar majalisar dokoki domin tabbatar da kammala manyan kwangiloli a fannin samar da lantarkin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya danganta rashin wutar lantarki mai kyau a Najeriya da cin hanci a bangaren samar da wutar.
Ola Olukoyede ya ce 'yan Najeriya za su cika da mamaki idan har har aka bayyana sakamakon binciken da EFCC ta gudanar a fannin wutar kasar.
Hukumar EFCC ta gano rashawa a fannin lantarki
Yayin ziyarar kwamitin majalisar tarayya kan yaki da rashawa, Olukoyede ya nuna damuwa game da lalatattun kayayyakin da ake amfani da su, inji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban na EFCC ya bayyana cewa yawancin masu kwangiloli suna amfani da kayan aiki marasa inganci, wanda ke jawo lalacewa da yawan durkushewar wutar.
Mista Olukoyede ya ce binciken da EFCC ta yi ya gano cewa 'yan kwangila kan sayo kaya marasa inganci, wanda a karshe ke jawo matsala ga samar da wutar.
EFCC ta nemi a karasa kwangilolin lantarki
Ya jaddada cewa irin wannan abu yana cikin manyan dalilan da ke haifar da rashin wuta mai dorewa a Najeriya, kamar yadda EFCC ta wallafa a shafinta na Intenet.
Ola Olukoyede ya bayyana cewa akwai fiye da kashi 20 cikin 100 na ayyukan manyan kwangiloli da ba a kammala ba a cikin shekaru 20 da suka gabata.
A cewarsa, rashin kammala ire iren wadannan ayyukan da ke da matukar amfani na hana ci gaban ababen more rayuwa da cigaban Najeriyar baki daya.
EFCC ta nemi hadin kan majalisar tarayya
Olukoyede ya nemi hadin kai daga majalisar tarayyar domin tabbatar da an kammala ayyukan manyan kwangiloli zuwa akalla kashi 50.
Hukumar EFCC ta ce ta karɓi sama da korafe-korafe 17,000 da suka shafi rashawa kuma tana gudanar da bincike kan fiye da laifuffuka 20,000 a fadin kasar.
Shugaban kwamitin majalisar, Obinna Onwusibe, ya bukaci EFCC ta yi aiki da bangaren shari’a domin saurin yanke hukunci da rage cunkoso a gidajen yari.
'Yan Najeriya sun fusata da lalacewar wuta
A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan Najeriya da dama sun mamaye kafafen sada zumunta domin nuna bacin ransu kan sake durkushewar tashar lantarki.
Bayan sanarwar durkushewar tashar da gwamnati ta fitar, Legit Hausa ta zanta da wasu 'yan Arewa, inda suka aika sako ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng