Masu Zanga Zanga Sun Mamaye Ma'aikatar Kudi a Abuja, Sun Nemi a Ba Su Hakkinsu
- Wasu gungun ƴan fansho sun yi wa ma'aikatar kudin tarayya tsinke don nuna fushinsu kan rike hakkokinsu na tsohon tsarin fansho
- Masu zanga-zangar sun bukaci gwamnati ta gaggauta biyansu kuɗinsu wanda aka tara masu a tsoron tsarin kafin a canza a 2004
- Shugaban kungiyar ƴan fansho, Kwamared Sylva Nwaiwu ya ce gwamnati ta gaza biyan ma'aikatan da suka ajiye aiki a 2003 hakkinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Tsofaffin ma'aikatan gwamnatin tarayya da ke karɓar fansho sun mamaye ma'aikatar kuɗi ta tarayya da ke Abuja kan rashin biyansu hakkinsu.
Masu zanga-zangar sun yi kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta biyansu kuɗaɗensu da aka rike na tsawon lokaci.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa shugaban kungiyar ’yan fansho ta kasa, Kwamared Sylva Nwaiwu ne ya jagoranci masu zanga-zangar zuwa ma'aikatar kudi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin zanga-zangar ƴan fansho a Abuja
Jagoran masu zanga-zangar, Sylva Nwaiwu ya yi kira da a gaggauta sakar masu kudaden da aka tara da nufin za a ba su idan sun gama aiki.
Wannan kuɗaɗe da masu zanga-zangar ke magana a kansu suna karkashin tsohon tsarin fansho ƙafin gwamnatin tarayya ta kirkiro sabo a shekarar 2004.
A bisa tanadin dokar, duk wani haƙkin fansho kafin sabon tsarin da aka kawo a 2004, za a biya su kai tsaye zuwa asusun fanshon kowane ma'aikacin gwamnatin tarayya.
Ƴan fansho sun koka wajen zanga-zanga
Da yake jawabi, jagoran masu zanga-zangar, kwamared Nwaiwu ya ce galibin ma'aikatan da suka yi ritaya tun 2003 ba a biya su haƙƙinsu ba.
Ya koka da cewa gwamnatin tarayya ta riƙe haƙƙoƙin ƴan fanshon, har yanzu ba a tura masu zuwa asusun ajiyar ba, kamar yadda The Nation ta kawo.
Gwamnati ta yiwa ƴan fansho ƙari
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ma'aikatan da suka yi ritaya daga aikin gwamnati za su samu karin kudin fansho da N32,000.
Gwamnatin ta bakin hukumar NSIWC ta ce karin kudin fanshon ya biyo bayan aiwatar da sabon mafi karancin albashi da aka yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng