Gwamna Ya Bayyana Gaskiya kan Batun Tashin Bam a Babban Birnin Jihar Arewa
- Gwamnatin jihar Plateau ta kwantar da hankalin mutane kan batun dasa wani abin fashewa a birnin Jos
- Caleb Mutfwang ya ce ko kaɗan babu barazanar dasa abin fashewa a kusa a tsohon asibitin koyarwa na jami'ar Jos (JUTH)
- Ya buƙaci mutane da su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum sannan su kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba ga jami'an tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Plateau - Gwamnan jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya yi magana kan jita-jitar da aka yaɗa ta tashin bam a birnin Jos.
Gwamna Mutfwang ya yi watsi da jita-jitar da aka yaɗa kan zargin dasa wani bam a tsohon asibitin koyarwa na jami’ar Jos (JUTH) kusa da kasuwar Terminus a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.
A wata sanarwa da daraktan yaɗa labaransa, Gyang Bere, ya sanyawa hannu, gwamnan ya bayyana cewa batun dasa bam ɗin ƙarya ne, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me gwamnan Plateau ya ce kan dasa bam?
Ya bayyana cewa an fara jita-jitar ne bayan wasu gungun mutane sun yi wa wani tarin ledoji fassarar cewa bam ne, rahoton Daily Post ya tabbatar.
Ya ƙara da cewa rahoton nasu ya haifar da fargaba da firgici a tsakanin al’ummar yankin.
Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa, jami’an tsaro da suka haɗa da tawagar ƴan sanda masu duba bama-bamai sun mayar da martani cikin gaggawa, inda suka gudanar da cikakken bincike a wurin.
Bayan gudanar da cikakken bincike, ba a samu shaidar wani abu mai fashewa ba a wurin.
Gwamna Mutfwang ya ba da shawara
Gwamna Mutfwang ya yi kira ga al’umma da su mai da hankali wajen goyawa manufofin gwamnati baya na samar da dawwamammen zaman lafiya.
Ya kuma ja hankalin jama'a musamman na kusa da ƙasuwar Terminus da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da tsoro ba, kuma su gaggauta kai rahoton duk wani abin zargi ga jami'an tsaro.
Gwamna Mutfwang ya kori ciyamomi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Plsteau Caleb Mutfwang ya sallami dukan shugabannin kananan hukumomi.
Gwamnan ya kori shugabannin rikon ne guda 17 da aka naɗa su a watan Yunin 2023 da zimmar yin wa'adin watanni shida.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng