Yadda Lakurawa Ke Sauya Limamai, An Gano Barazanar da Suke Yiwa Yan Bindiga

Yadda Lakurawa Ke Sauya Limamai, An Gano Barazanar da Suke Yiwa Yan Bindiga

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa yan kungiyar Lakurawa sun mamaye yankuna da dama a jihar Sokoto
  • Hadimin shugaban karamar hukumar Tangaza, Gazali Aliyu ya fadi irin ta'addancin da Lakurawa ke yi
  • Gazali ya musanta labarin cewa suna ba matasa N1m domin shiga kungiyar kamar yadda ake yadawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Hukumomi a jihar Sokoto sun bayyana irin ta'addancin da kungiyar Lakurawa ke yi na tsawon lokaci.

Hadimin shugaban karamar hukumar Tangaza a bangaren tsaro, Gazali Aliyu ya ce kungiyar ta dauki lokaci mai tsawo a jihar.

Yadda Lakurawa ke sheke ayarsu a jihar Sokoto
Hukumomi sun bayyana yadda Lakurawa ke sauya limamai a lokacin da suke so. Hoto: @ahmedaliyuskt.
Asali: Twitter

Lakurawa na yi wa yan bindiga barazana a Sokoto

Gazali ya bayyana haka ne yayin hira da jaridar DCL Hausa a yau Talata 12 ga watan Nuwambar 2024 da ta wallafa a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

"Lakurawa sun zo da shiri:" Bukarti ya ce yan ta'adda sun yi shekaru a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gazali ya ce Lakurawa sun yi kaurin suna inda suka yin barazana ga yan bindiga kan su bi su ko su bar yankin.

Ya bayyana yadda yan ta'addan ke kara yawa inda ya tabbatar da cewa farko ba su wuce mutane 50 ba.

Yadda Lakurawa ke sauya limamai a jihar Sokoto

"Gaskiya ƙungiyar Lakurawa ba maganar yau ko jiya ba ce saboda sun fi shekaru biyu zuwa uku a wannan yanki tun ba su wuce su 50 har sun kai 1,000."
"Lokacin da suka zo ko mota ba su da shi kuma ana ganinsu a lokacin ba su da yawa amma yanzu babu wanda zai iya fada maka yawansu."
"Abin takaici yanzu Lakurawa suna zuwa kauyuka suna kwace bindigogi a hannun yan sa kai na 'Community Guard'."
"Suna zuwa gari su gwada ilimin liman, idan bai ci ba, su ba shi kashi, su sauya shi da wani."

Kara karanta wannan

An samu bayanai kan sakon Lakurawa ga Bello Turji game da ayyukan ta'addanci

- Gazali Aliyu

Gazali Aliyu ya musanta labarin cewa suna ba matasa N1m domin shiga kungiyar inda ya ce ko N100,000 ba su gani ba.

Lakurawa za su aika sako ga Turji

Kun ji cewa shugaban kungiyar Lakurawa, Ameer Habib Tajje zai tura muhimmin sako ga dan ta'adda, Bello Turji.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Tajje zai aika sakon ne domin bukatar Bello Turji ya janye daga ayyukan ta'addanci da yake yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.