"Lakurawa Sun Zo da Shirinsu:" Bukarti Ya Ce Yan Ta'adda Sun Yi Shekaru a Najeriya

"Lakurawa Sun Zo da Shirinsu:" Bukarti Ya Ce Yan Ta'adda Sun Yi Shekaru a Najeriya

  • Mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Bulama Bukarti ya shawarci hukumomi su tashi tsaye wajen magance ayyukan Lakurawa
  • A yan kwanakin nan aka fara samun karuwar damuwa kan kungiyar da Bukarti ya ce ta riga ta yi karfi a jihar Kebbi wa bangarorin Arewa
  • Barista Abdu Bulama Bukarti ya nanata cewa akwai bukatar a yi da gaske domin kakkabe illar da Lakurawan za su shigo kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kebbi - Lauya da ke rajin kare hakkin dan Adam, Abdu Bulama Bukarti ya fallasa cewa yan ta’addan Lakurawa sun dade a Najeriya kafin yanzu.

Ya bayyana cewa mayakan Lakurawa sun dade da kwace iko da wasu garuruwa a jihar Kebbi inda su ka fara kafa sansaninsu.

Kara karanta wannan

Yadda Lakurawa ke sauya limamai, an gano barazanar da suke yiwa yan bindiga

Bukarti
Bulama Bukarti ya koka kan bullar Lakurawa Hoto: @ZagazOlaMakama/Abdu Bulama Bukarti
Asali: Twitter

Jaridar Aminiya ta wallafa cewa Bulama Bukarti ya kara da cewa sun samu bayanan yadda mayakan su ka shafe akalla shekaru shida a Kebbi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bulama Bukarti ya fadi illar Lakurawa

Abdu Bulama Bukarti ya bayyana cewa kungiyar Lakurawa ta fi ta mayakan Boko Haram da ISWAP hadari a Arewacin Najeriya duba da yadda su ka mallaki makamai.

“Suna gina manyan sansanoni kuma da mugayan makamai kuma har da jirage marasa matuki da suke amfani da su wajen yin sintiri a kan kauyuka da sansanonin sojin gwamnati.”

Bulama ya nemi a takawa Lakurawa burki

Mai fafutukar kare hakkin bil’adama, Bulama Bukarti ya shawarci hukumomin Najeriya da su tabbatar da an yi hobbasa wajen dakile ayyukan Lakurawa.

“Ya kamata a mayar da hankali a yi abin da ya kamata kan wannan lamari, domin ina tsoron nan ba da jimawa ba, za su sama babbar barazanar tsaro.”

Ya koka da cewa miyagun Lakurawan sun dade a jihar Kebbi, kuma babu karamar hukumar da babu su a halin yanzu

Kara karanta wannan

Wata 1 da birne matarsa, wani fitaccen dan wasan kwallon kafar Najeriya ya rasu

Lakurawa na son Magana da Turji

A baya mun ruwaito cewa shugaban kungiyar Lakurawa, Ameer Habib Tajje ya na son mika sako da ga jagoran kungiyar ta’addancin nan, Bello Turji kan ya tuba ya bar miyagun ayyukan da ya ke yi.

Manyan kasar nan, musamman a Arewacin Najeriya su na kuka da 'yan ta’adda, kuma sai aka samu bullar Lakurawa masu ra’ayin kungiyar Boko Haram da ta daidaita Arewacin kasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.