An Rantsar da Sabon Gwamnan Jihar Edo Tare da Mataimakinsa, Bayanai Sun Fito

An Rantsar da Sabon Gwamnan Jihar Edo Tare da Mataimakinsa, Bayanai Sun Fito

  • An rantsar da sabon gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo tare da mataimakinsa, Dennis Idahosa ranar Talata, 12 ga watan Nuwamba
  • Rantsar da gwamnan ya kawo karshen wa'adin mulkin Godwin Obaseki, wanda ya shafe shekaru takwas a madafun iko bayan Adams Oshiomhole
  • Okpebholo na jam'iyyar APC ya karɓi rantsuwar kama aiki ne bayan nasarar da ya samu a zaɓen gwamnan da aka yi a cikin watan Satumba, 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Sanata Monday Okpebholo ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon gwamnan jihar Edo bayan lashe zaben da aka yi a watan Satumba.

Wannan dai ya kawo karshen wa'adin tsohon gwamna, Godwin Obaseki wanda ya shafe shekaru takwas a kan madafun iko a jihar da ke Kudu maso Kudu.

Monday Okpebholo.
Monday Okpebholo na APC ya yi rantsuwar kama aiki Hoto: @EdoCommunity
Asali: Twitter

Tashar Channels tv ta tattaro cewa an gudanar da bikin rantsar da sabon gwamnan ne a yau Talata a filin wasa na Samuel Ogbemudia da ke birnin Benin, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna ya naɗa sabon SSG, ya ba ɗan tsohon shugaban APC babban muƙami

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Edo: An rantsar da gwamna da mataimakinsa

An rantsar da Gwamna Okpebholo tare da abokin takararsa, mataimakin gwamna a yanzu, Dennis Idahosa.

A jawabin da ya yi bayan rantsarwa, Okpebholo ya godewa al’ummar Edo bisa goyon bayan da suka ba shi wajen ganin ya zama gwamna.

Sabon gwamnan ya bayyana nasarar da ya samu da goyon bayan al'umma a matsayin dimokuradiyya, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Gwamnan Edo ya yi alkawarin riƙe amana

Gwamna Okpebholo ya ce:

“Bari in fara da gode wa Allah bisa ni’imominsa masu ban mamaki. A yau dai Dimokuradiyya ta sake farfaɗowa a jiharmu.” 
"A hukumance kun ba ni amanar jiharmu a matsayin gwamna na tsawon shekaru huɗu masu zuwa, ba zamu ci amanar da kuka damƙa mana ba ni da mataimaki na Hon. Dennis Idahosa."

Ya yi alkawarin inganta tsaro a jihar Edo, gina titunan zamani da za su haɗa garuruwa daban-daban, da tallafawa kananan ‘yan kasuwa domin habaka tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Gwamnan Edo ya dauki muhimmin alkawari bayan rantsuwar kama aiki

Edo: Gwamna ya yi naɗin farko kafin hawa mulki

A wani rahoton, kun samu labarin cewa Gwamna Monday Okpebholo, ya nada Fred Itua a matsayin babban sakataren yada labaransa.

Fred Itua, wanda ke da kwarewa mai yawa a aikin jarida, zai taimaka wajen inganta sadarwa tsakanin gwamnati da al’umma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262