An Soki Tinubu kan Wakiltar Najeriya a Taron Kasashen Musulmi da Larabawa
- Tsohon dan takarar shugaban kasa a APC, Cif Charles Udeogaranya ya caccaki shugaban kasa saboda zuwa taron Saudiyya
- Ana gudanar da taron kwanaki biyu wanda kasashen Musulmi da na Larabawa ke gudanarwa a Saudiyya domin tattauna matsalolinsu
- Cif Charles Udeogaranya ya caccaki Tinubu, inda ya zarge shi da karya dokar kasa wajen halartar taron domin bai shafi kasar ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon dan takarar shugaban kasa, Cif Charles Udeogaranya ya gargadi shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu kan wakiltar Najeriya a taron kasashen Larabawa da na Musulmi a Saudiyya.
Cif Udeogaranya ya bayyana haka ne a lokacin da Tinubu ke wakiltar kasar nan a kasar Saudiyya har ya fadi matsayarsa kan yakin da Isra’ila ke kai wa Gaza.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa shugaba Bola Tinubu ya take dokar kasa domin Najeriya ba musulmar kasa ba ce.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An caccaki Bola Tinubu kan taron Saudiyya
Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Cif Charles Udeogaranya ya fusata saboda yadda ya ce Bola Tinubu ya yi watsi da dokar kasa da ya rantse zai mutunta.
Ya ce babu wani dalili da zai ba Najeriya damar halartar taron da aka shirya saboda kasashen musulmi da larabawa da ake yi yanzu.
“Najeriya ba ta addini:” Tsohon dan takara
Charles Udeogaranya ya bayyana cewa Najeriya kasa ce da addini ba shi da tasiri a cikinta, saboda haka bai dace shugaba Bola Tinubu ya wakilce ta a matsayin musulma ba.
Ya kuma ce kasar nan ba balarabiyar kasa ba ce, saboda haka akwai tantama kan imanin Tinubu da kundin tsarin mulkin Najeriya.
Tinubu ya mika bukata Saudiyya
A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya mika bukatar Najeriya a taron kasashe Musulmi da na Larabawa da ke gudana a Saudiyya.
Bola Tinubu ya shaida matsayar Najeriya, inda ya bayyana cewa akwai bukatar a tsagaita harin da Isra’ila ke kai wa Falasdinawa inda dubban mutane su ka rasu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng