An Samu Bayanai kan Sakon Lakurawa ga Bello Turji game da Ayyukan Ta'addanci

An Samu Bayanai kan Sakon Lakurawa ga Bello Turji game da Ayyukan Ta'addanci

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa sabuwar kungiyar Lakurawa tana kokarin turawa Bello Turji sako kan ayyukan ta'addanci
  • An tabbatar da cewa shugaban kungiyar, Ameer Habib Tajje zai aike da muhimmin sako domin bukatar Turji ya bar ta'adin da yake yi
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake fama da ta'addancin Bello Turji, kwatsam sai ga shi Lakurawa sun bayyana a Sokoto da kewaye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Akwai rahotanni da ke nuna cewa sabuwar kungiyar ta'addanci, Lakurawa na shirin tura sako da Bello Turji.

Shugaban kungiyar, Habib Tajje zai tura muhimmin sako ga kasurgumin dan bindigan kan mugun ta'addanci da yake yi.

Shugaban Lakurawa zai tuntubi Bello Turji kan ayyukan ta'addanci
Shugaban Lakurawa, Ameer Habib Tajje zai tura sako ga Bello Turji kan janyewa daga ayyukan ta'addanci a Sokoto. Hoto: Legit.
Asali: Original

Yadda Lakurawa suka yi karfi a Sokoto

Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da haka ne a shafin X a jiya Litinin 11 ga watan Nuwambar 2024.

Kara karanta wannan

Sokoto: Kazamar fada ta barke tsakanin Turji da sojoji, bayan ganawa da basarake

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na zuwa ne yayin da kungiyar Lakurawa ke cigaba da addabar yankunan jihar Sokoto cikin yan kwanakin nan.

Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa yan ta'addan suna cigaba da yaudarar mutane da kuma karbar Zakka daga al'umma.

Lakurawa suna shirin tura sako ga Turji

Sanarwar ta ce Tajje ya dauki matakin tuntubar Bello Turji ne domin bukatar ya janye dukan ayyukan ta'addanci da yake yi a Arewacin kasar.

Sahara Reporters ta tabbatar da haka a cikin rahotonta inda ta ce Lakurawan sun fara karfi musamman a yankunan jihar Sokoto.

"A wani irin yanayi da ake ciki, shugaban Lakurawa, Ameer Habib Tajje zai tura muhimmin sako ga rikakken dan ta'adda, Bello Turji."
"Tajje zai tura sakon ne na musamman ga Turji domin bukatar ya janye daga ayyukan ta'addanci da yake yi a yankin Arewacin Najeriya."

- Cewar rahoton Zagazola Makama

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya karfafi yan Najeriya, ya yi kyakkyawan albishir

Bello Turji ya fafata da dakarun sojoji

Mun baku labarin cewa dan ta'adda, Bello Turji yana fafatawa da dakarun sojoji a yankin Bakin Gulbi da ke jihar Sokoto.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an fara fadan ne da misalin karfe 6.00 na safiyar yau Talata 12 ga watan Nuwambar 2024.

Hakan ya biyo bayan ganawar sirri da aka ce Bello Turji ya yi da wani dagaci a yankin da ke kusa da Gatawa a jihar Sokoto.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.