Yan Bindiga Sun Hallaka Wani Bawan Allah Ana Saura Ƴan Kwanaki Ɗaurin Aurensa
- Wasu ƴan bindiga da ake kyautata zaton ƴan kungiyar asiri ne sun kashe wani mutumi, Ɗanladi a jihar Edo da ke Kudu maso Kudu
- Wata majiya ta bayyana cewa Ɗanladi na shirye-shiryen ɗaura aurensa wanda za a yi a watan Disamba kafin wannan lamarin ya faru
- Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan Edo, Moses Yamu ya ce suna bakin ƙoƙarinsu wajen magance matsalar kungiyoyin asiri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Edo - Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne sun kashe wani mutumi da aka shirin daurin aurensa a watan Disamba a jihar Edo.
An ruwaito cewa matashin mai suna Ɗanladi a taƙaice ya rasa ransa ne a shagon abokinsa wanda bai wuce mita 100 ba daga caji ofis na Esigie ba.
Jaridar Premium Times ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a yankin ƙaramar hukumar Oredo a jihar Edo da ke Kudu maso Kudancin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan bindiga sun kashe mai shirin zama ango
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce Danladi na zaune a shagon, kwatsam aka zage gilas a wata mota kirar GLK Benz SUV aka harbe shi sau biyu da bindiga.
"Danladi mutum ne mai saukin kai, ɗa ne ga sarkin Hausawa a yankin. Kashe shi ba ƙaramar illa ba ce ga ƴan uwansa kuma matar da zai aura za ta ji raɗaɗin rashinsa.
"Har ya fara rabawa mutane katin gayyata zuwa ɗaurin aurensa, an sa masa ranar aure da masoyiyarsa a watan Disamba mai zuwa," in ji majiyar.
Yan sanda suna iya bakin kokarinsu
Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Edo, Moses Yamu, ya nuna danuwa da kashe-kashen da ‘yan kungiyar asiri ke yi a jihar.
A rahoton The Nation, Yamu ya ce:
"Yan sanda na iya bakin kokarinsu don ganin an kawo karshen ayyukan ƴan ƙungiyoyin asiri a jihar Edo."
Kakakin ƴan sandan ya buƙaci ɗaukacin al'umma a taimaka masu da bayanan sirri domin kawar da duk wasu miyagun laifuka masu alaƙa da ƙungiyoyin asiri.
Yan sanɗa sun kama rikakkun masu laifi
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sanda a jihar Edo ta tabbatar da kama wasu mutane hudu da ake zargi sun yi fashi da makami a gidan wani mutum.
Bayanan yan sanda sun tabbatar da cewa an yi fashi da makamin ne a Ibie ta Kudu a karamar hukumar Etsako ta Yamma a Edo.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng