Daurarru Sun Ji Labarin Matsin Rayuwa a Waje, An Samu Masu Murna da Zaman Kurkuku

Daurarru Sun Ji Labarin Matsin Rayuwa a Waje, An Samu Masu Murna da Zaman Kurkuku

  • Hadimin tsohon gwamnan Sakkwato, Shafi'u Umar Tureta ya bayyana yadda a sanar da mazauna kurkuku halin da kasa ke ciki
  • Kotun majistare ta aika Tureta, tsohon hadimin gwamna Aminu Waziri Tambuwal kurkuku bisa zargin zin zarafin gwamna Ahmed Aliyu
  • Tsohon hadimin ya ce wasu daga cikin mazauna gidan yarin suna cewa su na ji dadin yadda su ke iya cin abinci a kullum a daure

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto – Shafi’u Umar Tureta, tsohon hadimin gwamnan Sakkwato ya bayyana yadda ya tarar da mazauna gidan yari.

Shafi’u Tureta ya bayyana yadda ya rika ba daurarrun gidan yarin labarin irin halin da kasa ke ciki na tsadar rayuwa da hauhawar farashi.

Shafi'u Umar Tureta
Daurarru sun yi murna da zaman kurkuku saboda abinci Hoto: Shafi'u Umar Tureta
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, tsohon hadimin gwamnan Sakkwaton ya bayyana cewa masu karamin karfi da ke daure a gidan yarin sun yi ta godewa Allah SWT da ya kaddara zamansu a can.

Kara karanta wannan

Sanata ya ga halin da talakawa ke ciki, ya nemi mafita daga shugaba Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ra’ayin mazauna kurkuku kan tsadar rayuwa

Shafi’u Umar Tureta ya bayyana yadda mazauna gidan yari su ka rika murnar yadda su ke iya samun abin kai wa bakin salati a kullum.

Ya ce mutumin da ya ba labarin halin da kasa ke ciki karkashin mulkin Tinubu ya shaida masa cewa ko da babu dadi, ya na samun abinci a kullum, kuma wannan ma abin godiya ne.

An yi wa Tureta martani kan zaman kurkuku

Masu bibiyar shafin Shafi’u Umar Tureta a Sahar Facebook sun yi mamakin abin da ya sa bai yi zamansa a gidan yarin ba tun da akwai tsadar rayuwa a waje.

Sai dai ba dukkanin masu bibiyar shafin ne ke da irin wannan ra’ayi ba, wasu na ganin gwamnatin APC ta jefa jama’a cikin tashin hankali.

Yusuf Abdul Bube ya ce:

“Yanzu haka ma wasu idan yunwa ta ishe su laifi sukeyi a kais u gidan Dankande saboda abinci kyauta.”

Kara karanta wannan

'Ka hana Wike, gwamnoni ba alkalai motoci da gidaje,' SERAP ta fadawa Tinubu

Kotu ta ingiza Tureta kurkuku

A wani labarin kun ji cewa wata kotun Majistare da ke zamanta a Sakkwato ta aika hadimin Aminu Waziri Tambuwal gidan kurkuku bisa zargin cin zarafin gwamna Ahmed Aliyu.

An gurfanar da matashin a gaban kotu ne bisa zargin wallafa bidiyon mai dakin gwamna, Fatima Ahmed Aliyu ta na bushasha yayin bikin zagayowar ranar haihuwarwata da kuma kokarin cin zarafin gwamnan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.