Sarakuna Sun Haɗa Kai, Sun Tunkari Bola Tinubu kan Tsadar Rayuwa

Sarakuna Sun Haɗa Kai, Sun Tunkari Bola Tinubu kan Tsadar Rayuwa

  • Sarakunan gargajiya a jihar Delta sun yi magana da murya daya ga gwamnatin Bola Ahmed Tinubu kan halin wahalar rayuwa da ake ciki
  • Mai magana da yawun sarakunan, Luke Kalanama VIII ne ya zanta da manema labarai bayan sun yi taro a masarautar Akugbene-Mein
  • Sarakunan sun yi kira ga gwamnati kan samar da mafita mai dorewa a kan ambaliyar ruwa da ta ke lalata gidaje da gonaki duk shekara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Delta - Sarakunan gargajiya a jihar Delta sun yi kira ga gwamnatin Bola Tinubu kan tsadar rayuwa a Najeriya.

Shugabannin gargajiyar sun koka kan yadda yan Najeriya ke fama da wahalar rayuwa saboda wasu tsare tsaren gwamnati.

Bola Tinubu
Sarakuna sun bukaci Tinubu ya sauya tsare tsare. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa sarakunan sun ja hankalin gwamnati a kan matsalar tsaro a Najeriya.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya kafe a kan bakarsa, ya sake tunzura gwamnatin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganar sarakuna kan tsadar rayuwa

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa sarakunan gargajiya a jihar Delta sun bukaci gwamnatin Bola Tinubu ta canja salon tafiya.

Sarakunan sun ce a halin da ake ciki yan Najeriya da dama sun shiga matsalar tattalin arziki mai muni.

Rahotanni sun nuna cewa iyayen kasar sun yi kira ga gwamnatin tarayya ne bayan wani zama da suka yi a fadar masarautar Akugbene-Mein.

"Muna kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo tsare tsaren da za su fitar da yan Najeriya daga kuncin rayuwa da suke ciki.
Mutane ba za su iya cigaba da rayuwa ba idan aka cigaba da samun hauhawar farashi, dole a samar da mafita domin dawo da Najeriya tafarki mai dorewa."

- Luke Kalanama VIII, kakakin sarakunan Delta

'A kawo karshen rashin tsaro' - Sarakunan Delta

Haka zalika, sarakunan sun bukaci Bola Tinubu ya dauki matakin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta addabi Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya karfafi yan Najeriya, ya yi kyakkyawan albishir

A cikin bayanan da suka fitar, sarakunan sun bukaci a kawo mafita ga matsalar ambaliyar ruwa da ta ke faruwa duk shekara.

Tinubu ya bukaci a kara hakuri

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga yan Najeriya da su kara hakuri kan halin wahalar rayuwa da suke ciki a halin yanzu.

Haka zalika gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu ya ce tabbas ana fama da wahalar rayuwa amma sun jajirce a kawo karshen matsalar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng