Kano: Ɗan Sarki Sanusi II Zai Samu Babbar Sarauta, an Gayyaci Al'umma Gagarumin Bikin

Kano: Ɗan Sarki Sanusi II Zai Samu Babbar Sarauta, an Gayyaci Al'umma Gagarumin Bikin

  • Sarki Muhammadu Sanusi II ya shirya bikin nada babban dansa sarautar Chiroman Kano a ranar Juma'a mai zuwa
  • Za a nada DSP Aminu Lamido Sanusi ne a ranar Juma'a 15 ga watan Nuwambar 2024 a fadar Sarki da ke Kofar Kudu
  • Sarkin Kano ya tabbatar da haka ne a cikin wata sanarwa da Magajin Garin Kano, Muhammad Nasiru Wada ya sanyawa hannu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya sake shirya bikin nadin sarauta a jihar ba a gama rigimar masarauta ba.

Sarkin Sanusi II ya gayyaci al'umma zuwa bikin nadin babban dansa, DSP Aminu Lamido Sanusi a matsayin Chiroman Kano.

Sanusi II ya shirya nada dansa sarautar Ciroman Kano
Sarki Muhammadu Sanusi II ya gayyaci al'umma zuwa bikin nada dansa, DSP Aminu Lamido Sanusi sarautar Ciroman Kano. Hoto: Sanusi II Dynasty.
Asali: Facebook

Sarki Sanusi II ya shirya nada dansa sarauta

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa a shafin Facebook da Magajin Garin Kano, Alhaji Muhammad Nasiru Wada ya sanyawa hannu.

Kara karanta wannan

Gwamna a Arewa ya dawo da kwamishinan da ya dakatar, an samu bayanai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce tana gayyatar al'umma da yan uwa da abokan arziki zuwa bikin a ranar Juma'a 15 ga watan Nuwambar 2024.

Za a gudanar da bikin ne a fadar Sarki Sanusi II da ke Kofar Kudu da misalin karfe 9.00 na safe.

"Bayan gaisuwa da fatan alheri, an umarce ni da in sanar da kai cewa ka shigo Masallacin gidan Sarki da ke Kofar Kudu a ranar Juma'a 15 ga watan Nuwambar 2024 da karfe 9.00 na safe."
"Mai Martaba, Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II zai nada ka sarautar Chiroman Kano a wannan rana."
"Muna fatan ka sanar da yan uwa da abokan arziki su zo su taya ka murnar wannan nadin sarauta da Mai Martaba Sarki zai yi maka."

- Cewar sanarwar

Masarautar Kano ta taya Chiroman Kano murna

Daga bisani masarautar ta yi amfani da damar domin taya DSP Aminu Lamido Sanusi murnar samun wannan sarauta.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare, gwamnati ta sanya ranar cefanar da kadarorin babban banki

Har ila yau, bayan taya shi murna, masarautar ta yi masa addu'a tare da yi masa fatan alheri kan wannan sarauta da ya samu.

Sarki Sanusi II ya shawarci alkalai

A baya, kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi magana kan halayen wasu daga cikin alkalai da ke hukuncin zalunci.

Sarki Sanusi II ya shawarci alkalan da su tabbatar da yin adalci a dukan hukunce-hukunce da za su yi ba tare da wariya ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.